Labarai
Gwamnatin Jigawa Za Ta Bada Lamunin Sama Da Naira Biliyan 3 Ga Hukumar Alhazan Jihar
Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da bukatar hukumar Alhazai ta jihar na naira biliyan uku da miliyan dari uku da sittin a matsayin lamuni daga gwamnatin jihar.
Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, bayan kammala taron majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse.
Ya bayyana cewa, majalisar ta amince da hakan ne don bai wa hukumar damar ajiyar kujeru 400 na maniyyatan jihar Jigawa domin gudanar da ayyukin Hajjin shekarar 2025.
A cewarsa, amincewar ta biyo bayan gamsuwar da Majalisar ta yi, bisa yadda hukumar Alhazai ta Jiha ta mayar da bashin Naira biliyan biyu da miliyan dari biyu da gwamnatin ta bata a shekarar 2024.
Haka zalika Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce majalisar ta amince da shigar da dukkan masu rike da mukaman siyasa a cikin shirin kula da liyafa na jihar, kamar yadda hukumar kula da lafiya ta jihar Jigawa JICHMA ta tanadar a doka mai lamba. 02 -2024, da nufin inganta harkokin kiwon lafiya a jihar da ma Najeriya baki daya kamar yadda sakataren gwamnatin jihar ya gabatar.
Ya ce majalisar ta kuma bada goyon baya ga amincewar da Gwamna Umar Namadi ya yi, na sakin Naira Miliyan Dari Biyu da Hamsin a matsayin wani asusun hadin gwiwa da hukumar UNICEF domin siyan kayan abinci mai gina jiki ga kananan yara marasa lafiya.
Ya kara da cewa, amincewar kuma wani bangare ne na kokarin gwamnatin Namadi na yaki da matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara a jihar, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta gabatar.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
