Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Sayen Gidaje 96 Daga Gwamnatin Tarayya

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Miliyan 853 domin sayen gidaje guda 96 daga gwamnatin tarayya.

Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Dutse.

A cewarsa, majalisar ta amince da sayen gidajen ne daga Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ta Tarayya.

Ya bayyana cewa sayen gidajen na da nufin magance matsalar matsuguni a cikin jihar, musamman ga ma’aikatan gwamnati da sauran waɗanda suka cancanta.

Ya ce shirin na daga cikin Ajandar Gwamna Umar Namadi 12, wadda ta ƙunshi babbar dabarar bunkasa gidaje da raya birane, domin samar da matsuguni mai kyau, rage gibin gidaje, da inganta rayuwar al’umma.

Wannan na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin na faɗaɗa damar samun gidaje masu araha da kuma kyautata jin daɗin jama’a.

Ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da kashe sama da Naira miliyan 914 domin ƙarin ayyuka a kan aikin gina hanyar Chuwasu zuwa Chakwaikwaiwa zuwa Zango Maje, wadda za ta haɗa da hanyar Yan Dutse zuwa Chori.

Sagir ya ce ƙarin ayyukan sun zama wajibi bayan ƙarin binciken fasaha da bitar aikin da aka gudanar, domin ƙara inganta ƙarfinsa da tsarin magudanan ruwa.

Ya ce majalisar ta ce sauyin da aka yi a cikin tsarin aikin zai tabbatar da cewa aikin ya cika ƙa’idojin da ake buƙata, tare da biyan buƙatun zirga-zirgar al’ummomin da za su amfana da shi.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, da wannan amincewar, jimillar kuɗin kwangilar aikin ta kai sama da Naira Biliyan 5.4. Yana mai cewa hanyar Chuwasu zuwa Chakwaikwaiwa zuwa Zango Maje muhimmiyar hanya ce ta karkara wadda aka tsara domin inganta haɗin kai tsakanin al’umma, sauƙaƙa jigilar amfanin gona,  ƙara samun damar isa kasuwanni, makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya, tare da bunƙasa tattalin arziƙi a yankin da abin ya shafa.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara