Labarai
Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke kara dakile karfin ruwan tare da toshe hanyoyin da yake kwarara.
Hukumar Kula da Kogin Benuwe (UBRBDA) ta bayyana a wata sanarwa cewa matsalar na ƙara tsananta, musamman ga al’ummomin da ke amfana da ruwan kogin, ciki har da aikin noman rani da Geriyo, wanda aka dogaro da shi domin ayyukan ban ruwa.

Binciken da aka gudanar a ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2026, da misalin ƙarfe 5 na yamma, ya nuna cewa matakin ruwa ya kai mita 1 da digo 43, yayin da yawan ruwan da ke kwarara ya kai ma’aunin mita 64 a sakan guda, adadin da aka bayyana a matsayin mafi ƙaranci da aka samu a lokacin rani.
Masana sun yi gargadin cewa idan kwararar ruwa na raguwa matuka, taruwar laka kan ƙara tsananta matsalar, lamarin da ke haddasa raguwar zurfin ruwa, toshe hanyoyin shigar ruwa, rage ƙarfin gudun gudun ruwan, da kuma barazana ga wadatar shi domin ban ruwa.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, matsalar na iya ƙara muni, tare da shafar wadatar ruwa da ayyukan noma a lokacin rani.
Domin shawo kan matsalar, an fara aikin zurfafa hanyoyin ruwan na musamman, ƙarƙashin kulawar Shugaban Hukumar kuma Babban Jami’in Gudanarwa, Dakta Mahmud Sanusi Mohammed.

A cewar hukumar, aikin zai fi mayar da hankali ne a wuraren da laka ta fi taruwa domin dawo da kwararar ruwa yadda ya kamata, da sauƙaƙa zirga-zirgar ruwa, da kuma samar da ruwa domin ban ruwa ba tare da haddasa wata matsalar ba.
Jami’ai sun bayyana cewa wannan mataki ne na kariya da aka ɗauka bisa sahihan bayanai na kimiyya, maimakon a jira matsalar ta tsananta kafin ɗaukar mataki.
Daga:Yusuf/Safiyah
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
