Kasuwanci
An Yi Kira Ga Gwamnati Da Masu Ruwa Da Tsaki Su Rungumi Sauye-Sauyen Kula Da Yara Ta Zamani
An yi kira ga gwamnatoci a matakai daban-daban da sauran masu ruwa da tsaki da su rungumi sabuwar manhajar “Children First Software (CFS)” domin inganta sa ido da kula da yaran da ke cikin mawuyacin hali a Najeriya.
Shugaban ƙasa na ƙungiyar masu kula da gidajen marayu da cibiyoyin kula da yara a Najeriya (ASOHON), Gabriel Oyediji, ne ya yi wannan kiran a Ilorin yayin gabatar da manhajar da kuma ƙaddamar da reshen Kwara na ƙungiyar.
Ya ce wannan fasaha za ta taimaka wajen inganta rajista, haɗin gwiwa da kuma tabbatar da gaskiya a harkar kula da yara marasa galihu a gidajen marayu.
Oyediji ya bayyana cewa shirin wani muhimmin mataki ne da zai sauya tsarin kula da yara a Najeriya gaba ɗaya.
Ya kuma amince cewa akwai ƙalubale kamar ƙarancin wutar lantarki, rashin kayan kwamfuta, ƙarancin ilimin fasaha da kuma rashin ƙwararrun ma’aikata da ka iya shafar aiwatar da shirin.
Ya ce wasu cibiyoyin kula da yara har yanzu ba su da isassun kayan aiki da horo da ake buƙata domin amfani da tsarin yadda ya kamata.
Sai dai ya ƙara da cewa ƙungiyar na ci gaba da wayar da kai da horar da ma’aikata domin su iya amfani da manhajar yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa za a tura masu ƙirƙirar manhajar zuwa jihohi daban-daban domin horar da ma’aikatan gidajen marayu kan yadda ake amfani da ita.
Haka kuma ya ce tsarin zai taimaka wajen adana muhimman bayanai da ka iya lalacewa idan aka samu gobara ko ambaliya, yana mai cewa bayanan da aka adana a intanet za su kasance har abada.
Ali Muhammad Rabi’u/Ilorin
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
