Labarai
Kungiyar Marayu Ta Yi Kira Ga Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Gina Wa Mata Cibiyar Koyan Sana’o’i.
Kungiyar Marayu ta Jam’iyyatu Tukaful Aytam ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna ta taimaka mata wajen gina cibiyar koyarda sana’o’i.
Shugabar kungiyar, Malama Rabi’atu Adam Isma’il ta yi wannan kiran a wurin taron rabawa Marayu Kayayyaki da ya gudana a harabar ofishin kungiyar dake Barnawa Kaduna

Ta ce samarda cibiyar zai taimaka wajen samarwa mata da matasa hanyar sana’o’i domin su dogara da kansu.
Har ila yau, ta ce samarda cibiyar zai taimaka wajen kawarda ayyukan shaye-shaye a tsakanin matasa da kuma rage radadin talauci a tsakanin al’umar yankin.
Da take tsokaci a wurin taron, shugabar kungiyar Nisa’us Sunnah dake Barnawa Kaduna, Malama Amina Namadi tace Kungiyar Jam’iyyatu Tukaful Aytam ta kwashe shekaru 14 wajen ayyukan kulada marayu ta hanyar tara taro-sisi a tsakanin mambobinta.
Ta kara da cewa, a haka kungiyar ta dauki alhakin kulada marayu 10 tun suna kanana har suka kai wani mataki ta hanyar sanyasu a makaranta da ciyarda su da tufatarda su tareda koya musu sana’o’in hannu.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin Hauwa Usman da Usman Bala, sun godewa Kungiyar bisa wannan yunkuri, tareda addu’ar samun daukaka don kaiwa ga babban matsayi.

Kayayyakin da kungiyar ta raba su ne, kayan abinci da masarufi ga marayunta 12, sai kuma kayan Sallah ga sauran marayu maza da mata 60.
Khadija Kubau
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
