Connect with us
[radio_player id="1"]

Fasaha

Shirin Uwargidan Shugaban Kasa Ya Fara Aiki A Arewacin Nijeriya

Published

on

Mutane masu lalurar nakasa su 100 za su amfana da shirin gwamnatin jihar Plateau na naira dubu 100 kowanensu domin bunkasa samarda abinci.

Uwargudan shugaban kasa Sanata Olureni Tinubu ta bayyana wannan gudummuwa a wane banagre na Shirin sabonta fata da ofishinta ke gudanarwa.

Wannan. Shirin dai na sabunta fata, ofishin uwargidan shugaban kasa ne ya fito da shi domin tallafawa mata da masu lalurar nakasa da kula da ilimin mata da lafiya da aikin gona da karfafa mudu gwiwa su Iya dogaro da kansu.

Uwargidan shugaban kasar Sanata Oluremi Tinubu Kuma shugabar wannan shirin ta fada wajen kaddamar shi a yankin arewa ta tsakiya cewa, an gabatar da Shirin a kowane yanki in Banda yankin kudu maso kudu da za a gabatar Nan gaba.

Uwargidan shugaban kasar wacce ta sami wakilcin uwargidan shugaban ma’aikatan fadar Shuganan kasa kuma daraktar Shirin karfafa al’umma Mrs. Salamatu Gbajabiamila, Sanata Tinubu ta za a raba naira miliyan 10 ga mata 20 daga yankin Arewa ta tsakiya domin su ma su Sami damar gudanar akin gona don su ciyarda kansu.

Don haka Tayi kira ga wadanda zasu amfana da shirin su kashe kudaden su ta hanyar da ta dace.

A jawabinta tunda farko, uwargidan gwamnan Jihar Plateau Mrs. Helen Mutfwang wacce ta sami wakilcin kwamishiniyar ma’aikatar ilimi mai zurfi Mrs. Kachallom Gang ta bayyana mata a matsayjn kashin bayan kowace al’umma don haka tayi kira ga sauran matan gwamnonin jahohi suma su aiwatar da irin wannan Shirin a jahohinsu.

A sakonnin su daban daban, uwargidan gwamnan jihar kwara kuma shugabar Shirin ta jahohin ta tsakiya Farfesa Olufolake Abdurrazak wacce ta Sami wakilcin uwargidan shugaban majalisar wakilai Hajiya Sa’adatu da Kuma gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang dukkanin su bakinsu ya zo daya wajen godiya ga uwargidan shugaban kasa Sanata Olufemi Tinubu saboda wannan tallafin nata ga masu lalurar nakasa da ke tsakanin al’umma

Daga cikin abubuwan DA aka gabatar wajen wannan Taron shi ne gabatar da cakin kudi naira miliyan 10 ga jahohin arewa ta tsakiya da birnin Abuja da zasu amfana da shirin.

A yankin Arewa Maso Gabas Kuwa, Sanata Tinubu ta mika cek na Naira miliyan goma ga wadanda su ne matan shugabannin shiri a jihohinsu domin ci gaba da rabawa mata manoma a shirin.

Uwargidan mataimakin shugaban kasa Hajiya Nana Kashim Shettima ta wakilci uwargidan shugaban kasar, ta roki wadanda suka amfana da su kara fadada ayyukan su na noma a fannin kiwon dabbobi, kiwon kifi ko kiwon kaji domin bayar da tasu gudummawar wajen samar da abinci na gida da kasa baki daya.

Ta bayyana kwarin gwiwar cewa shirin ba wai kawai zai canza rayuwar daidaikun wadanda suka ci gajiyar shirin ba ne, har ma zai taimaka wajen samar da wadataccen abinci a yankin Arewa maso Gabas.

A Arewa Maso Yamma Kuwa da aka gabatar a Birnin Kbbi, Uwargidan Shugaban kasa ta bayyana cewa shirin zai tallafa wa mata dari da arba’in a harkar noma da kudi naira dubu dari biyar kowacce kuma za a tallafa wa mutum dari daya masu bukata ta musamman da Naira dubu dari kowane.

Uwargidan kakakin majalisar wakilai Fatima Tajuddeen Abbas ta wakilce ta, ta ce shirin zai hada kai da ma’aikatar noma ta tarayya domin tabbatar da samar da abinci da kuma dorewar abinci a kasar.

Don haka ta bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kudin da kayan aikin da aka ba su ta hanyar tallafa wa a samarda abinci a kasar.

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasiru Idris, a nata jawabin, ta bada nata tallafa, inda ta tallafa wa kowane mutum dari da arba’in da suka amfana da injinan fanfo mai amfani da hasken rana sannan kowane mai bukata ta musamman da kayan abinci iri-iri.

Josiah Buzum/Dauda Iliya/Abdullahi Tukur/ Shafii Wababe

Labarai

Labarai6 hours ago

Jirgin Karshe Na Alhazan Jihar Kwara Ya Isa Kasa Mai Tsarki

Sahun ƙarshe na mahajjata 140 daga jihar Kwara, ciki har da jami’an NAHCON, da ya tashi daga filin jirgin sama...

Labarai14 hours ago

Arsenal Na Dab Da Daukar Dan Wasan Gaba Viktor Gyokeres

Kungiyar Arsenal na shirin ɗaukar ɗan wasan gaban Sporting CP, Viktor Gyokeres kamar yadda jaridar wasanni ta football365 ta ruwaito. Arsenal...

Labarai16 hours ago

Majalisar Wakilai Za Ta Gabatar Da Dokoki Biyar Don Gyara Bangaren Man Fetur

Majalisar Wakilai za ta gabatar da kudurori guda biyar da za su magance manyan kalubale da ke hana ingantaccen aiki...

Labarai17 hours ago

Jigajigan Jihar Kebbi Sun Bukaci Hadin Kan ‘Ya’yan Jam’iyyar APC

Sanatocin jihar Kebbi guda uku da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, tare da Ministan Kasafin Kudi da...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Jihar Neja Ta Jaddada Shirinta Na Yaki Da  Matsalar Tsaro 

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa ya zama wajibi ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da yaki da rashin...

Labarai1 day ago

Jihar Jigawa Za Ta Sayo Motoci 36 Ga Mambobin Kungiyar NURTW

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga  Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta...

Labarai2 days ago

Hare-Haren Isra’ila Ya Hallaka Aƙalla Mutum 38 A Gaza Cikin Rabin Sa’a

Akalla Falasdinawa 38 ne suka rasa rayukansu a wani jerin hare-haren jiragen yaƙin Isra’ila da aka kai a sassa daban-daban...

Fasaha2 days ago

Dalibai Makarantun Sakandare A Kwara Sun Karɓi Tallafin Karatu

Akalla dalibai marasa galihu 300 da ke makarantun gaba da sakandare daga zababbun al’ummomi a kananan hukumomin Edu/Patigi/Moro na jihar...

Fasaha2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Nanata Kudurin Koyawa Matasa Sana’o’in Hannu

Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na horar da matasa sana’o’i daban-daban a fadin kasar nan.   Sakataren Ma’aikatar Agaji da...

Ilimi2 days ago

Kwara Ta Kafa Tutar Hadin Kai Mai Mita 70 A Ilorin

Gwamnatin jihar Kwara ta kafa tutar hadin kai mai tsayin mita 70 a hukumance, wanda ke zama alamar “hadin kan...

Mafi Shahara