Fasaha
FUT MINNA Ta Zo Ta Biyu Tsakanin Jami’o’in Da Suka Sami Tallafin TETFUnd
Jami’ar Fasaha ta Tarayya ta Minna da ke jihar Neja ta zama ta biyu a cikin jami’o’in Najeriya a lambar yabo ta tallafin bincike na Asusun Bincike na Kasa NRF.
Tallafin wata dama bincike ce da aka kirkira a karkashin kulawar Asusun Tallafawa Manyan makarantu a Najeriya.
Shugaban jami’ar Farfesa Faruk Adamu Kuta ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana bude taron yini uku mai taken amfani da fasahar zamani wajen dorewar ci gaba da cibiyar kula da harkokin da suka shafi adanawa da tanatar da abinci ta Africa ta shirya a Minna Babban birnin Jihar Niger.
Wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban jami’ar bangaren harkokin karatu Farfesa Abdullahi Mohammed Shugaban jami’ar yace FUT Minna ba wai kawai an kirkiresu ba ne domin bada digiri amma dole ne su fito da gagarumin bincike wanda ke da tasiri kai tsaye a kan ci gaban Najeriya kuma shi ya sa aka fi ganin su a matsayin su.
Farfesa Hussaini Anthony Makun ya ce wannan fasahar Nanotechnology tana tasiri ga duk wani nau’i na ayyukan ɗan adam, da duk wani abu da kuke son amfani da shi don samfur kuna buƙatar ilimin. Don haka ya yaba wa Shugaban Hukumar FUT Minna kan tallafin da yake bayarwa don yin bincike. da ci gaba.
Shima da yake jawabi shugaban tawagar binciken Farfesa Jimoh Tijjani ya bayyana cewa kasashe kamar Masar, Kenya, Maroko da kuma Afirka ta Kudu sun yi nisa wajen samar da fa’ida da yawa daga bincike da karbuwa fasahar Nanotechnology na dogon lokaci.
A cewarsa hatta a majalisar dinkin duniya ta mayar da hankali ne kan muradun ci gaba mai dorewa, guda goma sha shida daga cikin su, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar da su ba su goyon baya wajen bunkasa binciken Nanotechnology a Najeriya wanda ya ce sun yi nisa.
A jawabin bude taron daraktan bincike da ci gaban FUT Minna Farfesa Moses Aderemi Olutoye ya bayyana taron bitar a matsayin wanda yazo a lokacin da ya dace musamman tare da malamai masu halarta irin su Farfesa Sabelo Mhlanga, wanda ya kafa babban jami’in gudanarwa na jami’ar Sabinono LTD Nelson Mandela na Afirka ta Kudu da kuma Mataimakin Farfesa Olushola. Sunday Ayanda, Sashen nazarin tsirrai da Masana’antu na Jami’ar Tarayya Oye Ekiti wanda zai gabatar da lekca
COV ALIYU LAWAL/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
