Kasuwanci
Tsohon Ministan Harkokin Waje Gambari Ya Ƙalubalanci Matasa Kan Zaman Lafiya Da Gina Ƙasa
Daga ALI MUHAMMAD RABIU
Tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Farfesa Ibrahim Gambari, ya yi kira ga matasan ƙasar da su rungumi tattaunawa, riƙon amana da shugabanci na gari domin magance ƙalubalen ƙasa da bunƙasa ci gaba mai ɗorewa.
Gambari ya ce Najeriya na buƙatar matasa masu iya warware saɓani cikin lumana, samar da sabbin dabaru da kuma fifita muradun al’umma a kan burin kansu.
Ya bayyana hakan ne a cikin saƙon fatan alheri da godiya da aka gabatar a madadinsa a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara, inda Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya da Tsare-tsare da Ƙungiyar Ɗaliban Nazarin Zaman Lafiya da Tsare-tsare suka karrama shi da lambar yabo ta Golden Olive Award.
Da yake jawabi ta hannun Kanar Ademola Lawal mai murabus, Farfesa Gambari ya ce makomar ƙasar ba ta dogara da takardun shaidar karatun matasa kaɗai ba, har ma da ɗabi’unsu, riƙon amana da jajircewarsu wajen yi wa al’umma hidima.
Ya buƙaci matasan Najeriya da su fahimci cewa shugabanci ba ya taƙaita ga samun muƙami ko sarauta, sai dai ya ta’allaka ne da niyyar yi wa al’umma hidima da bayar da gudummawa ga ci gabanta.
Da yake waiwayar rayuwarsa daga Bode Saadu da Malete a Jihar Kwara zuwa fagen diflomasiyya na ƙasa da ƙasa, Gambari ya buƙaci ɗalibai da kada su bari asalin inda suka fito ya zama shinge ga burinsu na cimma nasara.
Sai dai ya jaddada cewa dole ne a haɗa buri da ƙwarewa, kyawawan ɗabi’u da shiri mai kyau domin cin gajiyar damarmakin da ake samu.
Tsohon ministan ya kuma nuna muhimmancin zuba jari a fannin ilimi, bincike da horas da mutanen da za su jagoranci ayyukan samar da zaman lafiya a nan gaba.
Ya gode wa shugabancin jami’ar, malamai da ɗaliban ƙungiyar bisa karramawar, yana mai bayyana ta a matsayin wata gagarumar shaida ta doguwar alaƙarsa da Jihar Kwara.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai5 days agoJigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a
-
Labarai3 days agoNIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu
-
Labarai4 days agoGobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara
-
Labarai4 days agoShugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo
-
Labarai1 day agoINEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna
-
Labarai5 days agoZa a Gabatarda Zaben Kananan Hukumomi a 2027 a Kaduna
-
Labarai2 days agoAn Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki
