Labarai
AKCILS Ta Karrama Jami’in Tsaro Bayan Shekaru 22
Daga Khadijah Aliyu
Mukaddashin Shugaban Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci da Shari’a ta Aminu Kano (AKCILS), Dakta Ali Tamasi Mu’az, ya karrama wani jami’in tsaro na kwalejin, Malam Murtala Idris, bisa jajircewa, gaskiya da ƙwazon aiki.
An gabatar da lambar yabon ne yayin wani taro a kwalejin, wanda ya samu halartar mambobin hukumar gudanarwa, ma’aikata da jami’an tsaro.
Da yake gabatar da lambar yabon, Dakta Mu’az ya ce karramawar ta yi daidai da manufar gwamnatin jihar Kano ta ganowa da ƙarfafa ma’aikatan da ke nuna ƙwazo, gaskiya da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
Ya yaba wa Malam Murtala bisa gaskiya, ƙwarewa da sadaukar da kai, yana mai cewa ya sha ganin sa yana tsaye a bakin aikinsa cikin dare yana gudanar da aikisa yadda ya kamata. Ya kuma buƙaci sauran ma’aikata su yi koyi da halayensa.
Dakta Mu’az ya yaba wa dukkan jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da kira ga ma’aikata da su ba sashen tsaro haɗin kai domin inganta ayyukan kwalejin. Ya ce hukumar za ta ci gaba da karrama ma’aikatan da suka nuna ƙwazo da gaskiya.
Hukumar kwalejin ta karawa Malam Murtala matsayi, tare da ba shi kyautar naira 50,000 da takardar yabo. Daraktan Tsaro, Malam Farouk Muhammad, ya ce Malam Murtala ya shafe shekaru 22 yana yi wa kwalejin aiki ba tare gazawa ba.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
