Fasaha
Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa da girka na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana a cibiyoyin Fasahar Sadarwa (ICT) da ke faɗin jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan matakin da majalisar ta ɗauka.
Ya bayyana cewa aikin zai shafi cibiyoyin ICT da ke Marke, Auyo, Dutse, Kazaure, Lafiya Guri, Madobi Dutse, Malam Madori, Danzomo da Sule Tankarkar.
Sauran wuraren sun haɗa da Kaugama, Kafin Hausa, Garki, Miga, Birnin Kudu, Ringim, Bulangu da Kanya Babba da ke ƙaramar hukumar Babura, baya ga sauran wuraren da aka ware a cikin kwangilar.
A cewar kwamishinan, shirin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na samar da ingantacciyar wutar lantarki mai ɗorewa ga cibiyoyin ICT, rage dogaro da hanyoyin samar da wutar lantarki da aka saba, da inganta ayyukan fasahar zamani.
Ya ce ana sa ran girka na’urorin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana zai inganta gudanar da ayyukan cibiyoyin, rage tsaikon da ake samu sakamakon katsewar wutar lantarki da samar da yanayi mai kyau don koyon dabarun amfani da fasahar zamani, koyon sana’o’i da ƙarfafa matasa.
Alhaji Sagir ya ƙara da cewa aikin zai taimaka wajen gudanar da horarwa kan fasahar ICT da sauran ayyukan koyon ilimin fasaha, ta yadda jama’a, musamman matasa, za su samu damar koyon muhimman dabarun amfani da fasahar zamani.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
