Ilimi
Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yaba wa Ministar Harkokin Mata Kan Inganta Rayuwar Al’umma
Daga Aminu Dalhatu
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa Ministar Harkokin Mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, bisa jagoranci nagari da kuma ci gaba da jajircewarta wajen inganta rayuwa, zamantakewa da tattalin arzikin mata a fadin Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Sakatariyar Yada Labaran Uwargidan Gwamnan, Rabi Yusuf, ta fitar, ta ce bayan Babban Taron Ƙarfafa Mata na Ƙasa da Shekarar 2026 da aka gudanar a filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja, Uwargidan Gwamnan ta bayyana wannan shiri a matsayin wani gagarumin yunƙuri da ke da nufin sake mayar da matan Najeriya a matsayin ginshiƙin ci gaban ƙasa.

Ta ce ƙarfafa mata yana haifar da ƙarfafa iyalai da kuma ci gaban al’umma, tare da tabbatar da cewa Jihar Zamfara na ci gaba da jajircewa wajen fitar da kudade don inganta harkar ilimi, bunƙasa tattalin arziki da kuma shigar mata cikin shugabanci.
Uwargidan Gwamnan ta kuma yi kira ga mata a fadin Najeriya, musamman wadanda suka ci gajiyar shirin, da su yi amfani da tallafin da aka ba su cikin hikima a karkashin shirin Sabunta Kudurori na Renewed Hope Agenda.

Ta bayyana manufofin gwamnati a matsayin hanya mai inganci wadda za ta gina ƙasa mai haɗin kai, wadata da dogaro da kai.
Taron ya samu halartar mata sama da 35,000 daga bangarori daban-daban na siyasa, zamantakewa da al’adu, wanda ya nuna haɗin kai da kuma kira ga ci gaba da haɗa kai.

Manyan baki da suka halarci taron sun haɗa da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu; matar Shugaban Majalisar Dattawa, Mrs. Ekaette Unoma Akpabio; matar Kakakin Majalisar Wakilai, Hajiya Fatima Abbas Tajudeen; da kuma sauran uwargidannin gwamnoni da manyan masu ruwa da tsaki.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
