Labarai
‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Satar Limamai 6 A Zamfara
Daga Aminu Dalhatu
Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da sace wasu limamai shida a kan hanyar Dakko zuwa Damri, a Ƙaramar Hukumar Bakura ta jihar.
An sace limaman ne ranar Asabar, 12 ga watan Satumban 2026, lokacin da suke tafiya zuwa Talata Mafara.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 da rabi na safe, lokacin da wasu ’yan bindiga suka yi wa motar da limaman ke ciki kwanton bauna.
Ya ce bayan samun rahoton, jami’in ’yan sandan da ke kula da sashen Bakura ya tattara jami’an tsaro, ciki har da jami’an Sashen Yaki da Miyagun Laifuka, VCRU, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro gudanar da bincike a dazuzzukan da ke kewaye da wuraren da ake zargin ’yan bindigar sun nufa, domin kuɓutar da limaman da kama waɗanda suka aikata laifin.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Zamfara, CP A. M. Bello, ya umarci jami’an da ke aikin ceto da su ƙara ƙaimi tare da amfani da dukkan dabarun da suke da su domin kuɓutar da waɗanda aka sace.
Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su taimaka da sahihan bayanai cikin gaggawa, waɗanda za su taimaka wajen gano inda limaman suke, domin kuɓutar da su da kuma kamo waɗanda suka aikata laifin.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
