Connect with us

Labarai

Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur

Published

on

Daga Bello Wakili 

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar dattijo, ɗan kasuwa kuma tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, Alhaji Bamanga Muhammad Tukur, wanda ya rasu yana da shekaru 90.

Shugaban ya bayyana rasuwar Tafidan Adamawa a matsayin ƙarshen wani muhimmin babi a tarihin siyasa da tattalin arzikin Najeriya.

An haifi Alhaji Tukur a ranar 15 ga Satumba, 1935, kuma ya taɓa zama Babban Manajan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya daga 1975 zuwa 1982. Daga bisani ya shiga siyasa a lokacin Jamhuriya ta Biyu, inda aka zaɓe shi Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, wadda yanzu ta ƙunshi jihohin Adamawa da Taraba, a shekarar 1983.

Marigayin ya kuma shugabanci kamfanonin BHI Holdings da DADDO Group of Companies, sannan ya riƙe muƙamin Ministan Masana’antu na Tarayya daga 1993 zuwa 1995 a lokacin mulkin Janar Sani Abacha.

A matakin Afirka, Bamanga Tukur ya kasance Shugaban Zartarwa na African Business Roundtable da kuma Shugaban NEPAD Business Group, inda ya yi fafutukar bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka da haɓaka tattalin arziki ta hanyar kamfanoni masu zaman kansu.

Babanga Tukur ya kuma kasance Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa daga watan Maris na 2012 zuwa Janairun 2014.

Shugaba Tinubu ya bayyana shi a matsayin mutum mai karamci da mutunci, wanda ya yi imani da makomar Najeriya, yana mai cewa ƙasar za ta yi matuƙar kewar shawarwarinsa da jagorancinsa.

Shugaban ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, Masarautar Fombina, Gwamnati da al’ummar Jihar Adamawa, da kuma bangaren siyasa da kasuwanci a Najeriya da Afirka. Ya roƙi Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sanya shi a Aljannar Firdausi.

 

Fassara; Safiyah Abdulkadir 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara