Connect with us

Labarai

Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Nemi Karin Kujerun Hajji na 2027

Published

on

Jigawa, HuUsman Muhammad Zaria 

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta nemi karin kujerun aikin Hajjin 2027 daga Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), domin biyan bukatar masu niyyar zuwa aikin Hajjin daga jihar.

Shugaban Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Ya ce hukumar ta kammala sayarwa da rajistar kujerun Hajjin da aka ware mata, inda jami’an rajistar suka tabbatar da cewa an shigar da bayanan dukkan wadanda suka cika ka’idojin zuwa aikin Hajji cikin tsarin rajistar yanar gizo.

A cewarsa, nasarar rajistar ta nuna kokarin hukumar na tabbatar da tsarin rajista mai gaskiya, inganci da tsari.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce hukumar ta gabatar da bukatar karin kujeru ga NAHCON sakamakon yawan masu son zuwa aikin Hajji daga sassa daban-daban na jihar.

Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu an rufe kafar shigar da bayanan fasfo, yana mai cewa Kungiyar Shugabannin Hukumomin Hajji na Jihohi ta roki NAHCON da ta sake bude kafar.

Shugaban Hukumar, ya bayyana fatan cewa NAHCON za ta amince da bukatar, domin bai wa karin maniyyata aikin Hajji damar kammala bayanansu.

Ya yabawa ma’aikatan hukumar bisa jajircewa da kokarin da suke yi wajen gudanar da ayyukansu, tare da kira ga maniyyatan aikin Hajjin 2027 da su rika dogaro da bayanan da hukumar ta bayar kawai domin kauce wa yaɗa labaran karya.

Haka kuma, Labbo ya mika sakon ta’aziyya ga NAHCON bisa rasuwar ma’aikacinta a Ofishin na Shiyyar Kano, Marigayi Alhaji Salisu Gaya, wanda ya rasu ranar Juma’a, 11 ga Satumba, 2026.

Fassara: Safiyah Abdulkadir 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara