Labarai
Karamar Hukumar Gwarzo Ta Kaddamar da Sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya
A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya a matakin ƙasa, Karamar Hukumar Gwarzo ta kaddamar da sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) da aka gina a garin Dankado, da ke cikin gundumar Sabon Birni.
Taron kaddamarwar, wanda ke nuna wani sabon ci gaba a tsarin raya jama’a, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, da wakilan al’umma.
Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dakta Mani Tsoho Abdullahi, wanda Mataimakinsa, Alhaji Abdulmumin Garba Lakwaya, ya wakilta, ya tabbatar da jajircewar gwamnatin sa wajen tabbatar da cewa kowane yanki a cikin karamar hukumar na da damar samun ingantacciyar kiwon lafiya mai sauƙin samu da araha.
Ya yaba wa Kakakin Majalisar Dokoki ta Gwarzo, Ahmad Shehu Sabon Birni, da sauran kansiloli bisa hadin kai da jajircewarsu wajen aiwatar da muhimman ayyukan raya al’umma, yana mai cewa irin wannan haɗin gwiwa ita ce ginshiƙin ci gaban karkara mai dorewa.
A nasa jawabin, Ahmad Shehu Sabon Birni, ya bayyana sabuwar cibiyar lafiya a matsayin wata cibiya da za ta tallafawa jama’ar Dankado da makwabtansu. Ya jinjinawa karamar hukumar bisa mayar da hankali ga bangaren lafiya, tare da yin alkawarin ci gaba da ba da goyon bayan majalisa ga duk wani shiri da zai inganta rayuwar jama’a.
Shugaban sashen kula da kiwon lafiya na Gwarzo, Alhaji Tukur Makama, ya yaba da hangen nesa da jajircewar shugaban karamar hukumar wajen saka jari a fannin lafiyar jama’a. Ya ce sabuwar cibiyar za ta taimaka wajen rage mace-macen mata da jarirai, faɗaɗa rigakafi, da kuma samar da taimakon gaggawa ga al’umma cikin lokaci.
Shugabannin al’umma, ƙungiyoyin matasa da na mata, sun bayyana godiyarsu, suna mai cewa aikin ya zo a kan kari kuma ya dace da bukatun jama’a.
Rel/Khadijah Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
