Labarai
Tinubu Ya Tura Rundunar Musamman Domin Ceto Wadanda Aka Yi Garkuwa da Su a Oyo
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya amince da ɗaukar masu kula da dazuzzuka (Forest Guards) guda 1,000 a Jihar Oyo, tare da ba da umarnin tura wata ƙwararriyar rundunar ceto ta tsaro domin tabbatar da ceto ɗalibai da malamai da aka sace a Ƙaramar Hukumar Oriire ta jihar.
An bayyana waɗannan matakai ne yayin wata ziyara da wata babbar tawagar gwamnatin tarayya ta kai ƙauyukan Esiele da Yawota da ke Ogbomoso, bayan sace ɗalibai da malamai daga makarantu uku a ranar 15 ga Mayu.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ta isar da saƙon Shugaba Tinubu na alhini kan lamarin, tare da tabbatar wa mazauna yankin cewa za a yi amfani da dukkanin hanyoyin da ake da su domin tabbatar da kubutar da waɗanda aka sace cikin koshin lafiya.
Gbajabiamila ya ce Shugaban Ƙasar ya kuma ba da umarnin a miƙa buƙatar al’ummar yankin na samar da sansanin soji a yankin domin a yi la’akari da ita.
A cewarsa, aikin ceto zai kasance bisa sahihan bayanan sirri, tare da amfani da hanyoyin soji da na sulhu domin tabbatar da dawo da ɗaliban da malaman da aka sace lafiya.
Tawagar ta haɗa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu; Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun; da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Harkokin Sadarwa da Jama’a, Sunday Dare.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
