Labarai
NCFBP: Jigawa Ta Fara Shirin Tallafa wa Iyalai Marasa Ƙarfi da Abinci
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta amince da ƙaddamar da haɗin gwiwar sassa daban-daban na Shirin BankinAbinci ga Al’umma na Kasa, wato National Community Food Bank Program NCFBP, reshen shiyyar Arewa maso Yamma, wanda Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu za ta ƙaddamar a Cibiyar Kula da Lafiya ta Farko ta Gandun Sarki da ke Ƙaramar Hukumar Mallam Madori a jihar.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta ne ya bayyana hakan bayan taron Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
A cewarsa, an ƙirƙiri wannan shiri ne domin yaƙi da yunwa da kuma matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ga yara.
Ya ce shirin zai taimaka wajen rage matsananciyar matsalar rashin wadataccen abinci da ke addabar marasa ƙarfi a faɗin ƙasar nan, ta hanyar samar musu da damar samun abinci na wani ɗan lokaci cikin tsari.
Dakta Nura Ibrahim Kazaure ya bayyana cewa za a tantance waɗanda suka cancanci cin gajiyar shirin a cibiyoyin kula da lafiya na farko, inda za a ba su takardun shaidar karɓar tallafi domin fansar kayan abinci a bankunan abinci da aka ware.
Ya ƙara da cewa waɗanda aka fi mayar da hankali a kansu sun haɗa da iyalai masu yara ƙanana ‘yan ƙasa da shekara shida, da kuma mata masu juna biyu da masu shayarwa da ke fuskantar haɗarin rashin wadataccen abinci mai gina jiki.
Kwamishinan ya ce shirin zai kuma yi amfani da damar da ƙasar ke da ita ta fannin noma domin tabbatar da cewa yalwar amfanin gona ta isa ga waɗanda suka fi buƙatarsa.
Ya ce wannan shiri ya yi daidai da manufofi 12 na Gwamna Namadi, musamman wajen tabbatar da inganta rayuwar da samar da wadatacce kuma ingantaccen abinci a jihar.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa gwamnatin jihar ta kuma jajanta wa waɗanda guguwar iska da ruwan sama suka shafa a sassa daban-daban na jihar.
Majalisar ta kuma umarci Ma’aikatar Jin-ƙai da Harkoki na Musamman da ta gaggauta kai tallafi ga waɗanda lamarin ya shafa.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
