Labarai
Majalisar Dokokin Kaduna Ta Amince da Sabbin Dokoki kan Sauyin Yanayi da Haraji
Daga Shamsuddeen Mannir Atiku
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da wasu muhimman dokoki guda biyu da suka shafi sauyin yanayi da kuma tsarin haraji, domin inganta rayuwar al’umma da bunkasa tattalin arzikin jihar.
A bangaren sauyin yanayi, majalisar ta amince da kudirin doka na kafa Hukumar Ba da Shawara kan Sauyin Yanayi ta Jihar Kaduna, wadda za ta rika bai wa gwamnati shawarwari kan hanyoyin yaki da sauyin yanayi, kare muhalli, da kuma fuskantar kalubalen da ke tattare da sauyin yanayi.
Shugaban Majalisar, Yusuf Dahiru Liman, ya bayyana cewa sabuwar hukumar za ta taimaka wajen tsara matakan da za su rage illolin sauyin yanayi kamar ambaliya, fari, da kwararowar hamada, tare da jaddada muhimmancin hadin kan al’umma wajen kare muhalli domin inganta lafiya da rayuwa.
Da yake gabatar da rahoton kwamitin, Shugaban Kwamitin Muhalli da Albarkatun Kasa, Usman Danlami Stingo, ya ce hukumar za ta kuma taimaka wa jihar wajen samun tallafi daga kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa, tare da kula da dukkan batutuwan da suka shafi muhalli. Ya kara da cewa mambobin hukumar za su hada da wakilai daga hukumomin gwamnati, kungiyoyin farar hula, kungiyoyin addini da sauran masu ruwa da tsaki.

Usman Danlami Stingo, Shugaban Kwamitin Muhalli da Albarkarun Kasa na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna
A wani bangare kuma, majalisar ta soke Dokar Tattarawa da Tsara Haraji ta shekarar 2020, tare da kafa sabuwar Dokar Harajin Jihar Kaduna ta shekarar 2025.
Shugaban Majalisar ya ce sabuwar dokar ta tattara dukkan tanade-tanaden haraji cikin tsari guda domin saukaka fahimta da aiwatarwa, tare da kawar da maimaituwa da tsofaffin dokoki da suka daina dacewa da zamani.
Tun da farko, Shugaban Kwamitin Harkokin Kudi, Halliru Bello Dangana, ya bayyana cewa bayan nazari mai zurfi, kwamitin ya ga dacewar samar da sabuwar dokar da za ta hada dukkan nau’o’in haraji cikin kundin doka guda daya da aka sabunta.

Halliru Bello Dangana, Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna
Ya kara da cewa sabuwar dokar za ta taimaka wajen toshe hanyoyin asarar kudaden haraji da kuma kara yawan kudaden shiga na jihar, wanda hakan zai tallafa wa ayyukan ci gaba da gina ababen more rayuwa.
Majalisar ta jaddada cewa wadannan dokoki biyu za su taka muhimmiyar rawa wajen inganta muhalli da kuma karfafa tattalin arzikin Jihar Kaduna.
-
Labarai4 days agoRukunin Farko na Maniyyatan Jihar Jigawa Ya Tashi Zuwa Kasar Saudiyya
-
Labarai2 days agoJihar Jigawa Ta Kammala Jigilar Alhazai Zuwa Kasa Mai Tsarki
-
Labarai4 days agoRukunin Farko na Alhazan Jihar Kebbi ya Isa Kasa Mai Tsarki
-
Kasuwanci2 days agoBOA da Majalisar Wakilai za su Samar da Injinan Noma a Dukkan Mazabu
-
Labarai5 days agoKashim Shettima Ya Kaddamar da Jirgin Farko na Maniyyatan Najeriya
-
Labarai2 days agoGwamna Bago Ya Umurci SEMA Ta Gaggawata Kai Tallafi ga Wadanda Iftila’in Guguwa ya Shafa a Mokwa da Bida
-
Ilimi2 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yaba wa Ministar Harkokin Mata Kan Inganta Rayuwar Al’umma
-
Labarai4 days agoGwamnan Jigawa Ya Bukaci Alhazai Su Yi Addu’ar Zaman Lafiya da Ci Gaban Najeriya
