Fasaha
Majalisar Jihar Kano ta Bukaci Gwamnati ta Kafa Cibiyoyin ICT
Daga Khadijah Aliyu
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar da ta kafa cibiyoyin jarabawa da ake amfani da na’urar kwamfuta (CBT) a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar, domin dacewa da sabon tsarin jarabawar kammala sakandare WAEC da NECO.
An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa a zaman majalisar wanda Kakakin Majalisar, Jibril Falgore, ya jagoranta.
Wannan kudiri ya fito ne daga dan majalisa mai wakiltar mazabar Madobi kuma Shugaban Kwamitin Ilimi na Majalisar, Mukhtar Ishaq.
Ya bayyana cewa sabon tsarin ya wajabta gudanar da jarabawa ta hanyar kwamfuta, yana mai jaddada bukatar gaggauta bai wa dalibai kwarewar amfani da na’urar ta kwamfuta.
A cewarsa, kafa cibiyoyin kwamfuta (ICT) a fadin jihar zai taimaka wajen rage gibin fasahar zamani tare da shiryawa dalibai a birane da karkara domin fuskantar jarabawar ta CBT.
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Shanono/Bagwai, Ali Lawan, ya goyi bayan kudirin, yana mai cewa lokaci ya yi kuma abu ne mai matukar muhimmanci.
A wani labarin kuma, Majalisar ta bukaci gwamnatin jihar da ta kammala ayyukan samar da wutar lantarki a garuruwan Garun Madadi da Yarguruza da ke karamar hukumar Gwarzo.
Wannan kudiri ya fito ne daga Yunusa Haruna, wanda ya jaddada cewa an riga an zuba kudade masu yawa a aikin, kuma kammala shi zai taimaka wajen magance matsalolin wutar lantarki da ake fama da su.
Da yake goyon bayan kudirin, Sule Lawan Shuwaki mai wakiltar Tudun Wada ya ce kammala aikin zai bunkasa harkokin tattalin arziki a yankin.
Haka kuma, Majalisar ta karbi rahoto kan kudaden Majalisar Masarautar Rano na shekarun 2023–2024, sannan ta amince da kudirori kan gyaran Dam din Buda a Garko da kuma gina hanya a Makoda.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
