Connect with us

Ilimi

Ilimi Shi ne Ginshikin Cigaban Al’umma- Gwamna Namadi

Published

on

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jaddada ilimi a matsayin ginshikin ci gaban jihar da makomarta.

Ya bayyana haka ne a bikin yaye dalibai karo na biyu na  Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa, inda aka yaye dalibai daga zangon karatu na shekarar  2018/2019 zuwa 2024/2025.

Gwamnan ya ce babu wani fanni da ya fi ilimi muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaba mai dorewa.Ya taya daliban da suka kammala karatu murna tare da yabawa kokarin shugabannin jami’ar da suka taka rawa wajen ci gabanta tun bayan kafuwarta.

Namadi ya bayyana cewa gwamnatinsa na bai wa ilimi muhimmanci sosai, inda take ware tsakanin kashi 26 zuwa 30 cikin dari na kasafin kudin jihar ga bangaren ilimi, lamarin da ya taimaka wajen inganta gine-gine, koyo da koyarwa, da kuma kara yawan masu shiga makaranta tare da rage yara marasa zuwa makaranta.

Ya kuma ce an mayar da wasu manyan makarantun sakandare cibiyoyin kwarewa domin bunkasa ilimin sana’o’i, tare da kokarin da ake yi na daidaita Kwalejin Babura da tsarin TVET na kasa, domin karfafa ilimin fasaha.

A bangaren ilimin gaba da sakandare, gwamnan ya bayyana cewa jihar ta karbe wata jami’a mai zaman kanta a Majia da ke karamar hukumar Taura, inda ake shirin mayar da ita jami’a ta musamman kan fannin kiwon lafiya da sauran fannoni masu alaka.

Ya ce an riga an kammala matakan tantancewa, yayin da kudirin dokar tabbatar da wannan sauyi ke gaban majalisar dokokin jihar domin amincewa.

Gwamnan ya kuma lissafo wasu manyan ayyuka da ake yi a Jami’ar Sule Lamido, ciki har da gina Kwalejin Kiwon Lafiya, dakunan kwanan dalibai da gidajen ma’aikata.

Sauran ayyukan sun hada da gina gidajen malamai, cibiyar binciken harkar noma da kuma sabon filin taron yaye dalibai.

Jimillar dalibai 4,109 ne aka ba shaidar digirin farko a bikin, wanda ya nuna yadda jami’ar ke ci gaba da habaka a fannin ilimi a cikin shekaru kalilan.

Haka kuma, an nada Sarkin Katagum, Alhaji Umar Faruk na II, a matsayin Uban Jami’ar na biyu, tare da bai wa wasu fitattun mutane uku digirin girmamawa a yayin bikin.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara