Labarai
Namadi Ya Kaddamar Da Gina Sabuwar Fadar Sarkin Dutse
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana gina sabuwar fadar Sarkin Dutse a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaban Masarautar Dutse da jihar baki ɗaya.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka ne a wajen bikin aza harsashin ginin fadar a Dutse, babban birnin jihar.
Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ya wakilta, ya tabbatar da cewa za a gudanar da aikin bisa inganci.
Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Nuhu Muhammadu Sunusi, ya bayyana farin cikinsa da fara aikin, yana mai cewa marigayi mahaifinsa, tsohon Sarkin Dutse, Dr Muhammadu Muhammadu Sunusi, yana da burin ganin an gina sabuwar fadar.
Sarkin ya gode wa Gwamna Umar Namadi bisa cika wannan buri, yana mai bayyana fadar a matsayin gida ga daukacin al’ummar Jihar Jigawa. Ya kuma yaba wa malamai da shugabannin ƙananan hukumomin Masarautar Dutse bisa goyon bayan da suke bayarwa.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dutse, Dr Abubakar Sani Birnin Kudu, ya jagoranci addu’o’i na musamman a wajen bikin, kafin Sarkin Dutse da wakilin Gwamnan su jagoranci aza harsashin ginin.
Sabuwar fadar da ake ginawa kusa da babban Masallacin Juma’a na Dutse, kusa da Jami’ar Tarayya ta Dutse, ana sa ran kammala ta cikin watanni 18.
Taron ya samu halartar sarakuna, shugabannin ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki.

Fassara : Safiyah Abdulkadir
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
