Connect with us

Labarai

Za a yi makonni kafin tantance waɗanda gobarar jirgin ruwan Philippine ta shafa

Published

on

Masu aikin ceto

Asalin hoton,AFP via Getty Images

Hukumomi a Philippine sun ce za a iya ɗaukan makonni ko ma watanni kafin tantance mutanen da gobarar jirgin ruwa ta shafa a makon da ya gabata.

Lamarin dai ya yi sanadin mutuwar mutum 76.

“Akasarinsu sun ƙone sosai,” in ji Richard Allan Mangalip, wani ƙwararren jami’in bincike a hukumar ƴansandan Philippine.

An nemi iyalan mutanen da su taimaka wajen tantance su ta hanyar gwajin DNA da kuma wasu kayayyaki da suka mallaka.

Jirgin ruwan ƙirar MV June Aster ya nufi Coron ne daga Manila a Lardin Palawan, wani fitaccen wajen zuwa hutu, a lokacin da gobarar ta tashi ta inda ake ajiye kaya sannan kuma ta yaɗu zuwa sassan jirgin.

Mutum 43 ne suka tsira yayin da wasu 13 kuma har yanzu ba a san inda suke ba, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Jami’in ya ce suna ta ƙoƙarin abubuwan da za su taya su tantance mutanen sai dai a cewar shi zai yi wuya a iya bayar da wa’adi na tsawon lokacin da za a ɗauka na tantancewar – “zai iya kai wa makonni, ko ma watanni”.

Wani jami’in tsaron teku, a ranar Asabar, ya ce abin da suka bai wa muhimmanci a yanzu shi ne tantance mutanen da kuma gano musabbabin gobarar.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara