Ilimi
Zamfara Ta Kara Hutun Makaranta Zuwa Makonni Biyu Saboda Cutar Mashako
Daga Aminu Dalhatu, Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara ta daga ranar komawar ɗalibai makaranta a duk makarantun gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar da makonni biyu, bayan shawarwarin hukumomin lafiya dangane da halin da ake ciki na cutar mashako
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Abdulmalik Abubakar Gajam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar kan cutar.
Ya ce an ɗauki wannan matakin ne domin kare lafiya da jin daɗin ɗalibai da malamai da sauran al’ummar makarantu.
A cewarsa, tsawaita hutun zai ba hukumomin lafiya da na ilimi ƙarin lokaci domin ƙarfafa sa ido kan cutar tare da gano mutanen da suka yi mu’amala da masu cutar da tantance bayanan allurar rigakafi da wayar da kan jama’a da kuma ɗaukar wasu matakan kariya kafin a sake buɗe makarantu.
Kwamishinan ya umurci dukkan masu makarantu da shugabannin makarantu da hukumomin kula da makarantu da su bi umarnin kara kwanakin hutun.
Ya kuma buƙaci makarantu su yi amfani da wannan lokacin wajen tsaftace makarantunsu ta amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta a harabar makarantu yadda ya kamata, da kuma tabbatar da samar da isassun wuraren wanke hannu.
An kuma shawarci iyaye da masu kula da yara da su ba hukumomin lafiya haɗin kai wajen allurar rigakafi da tantance lafiyar yara da sauran matakan kariya da aka ba da shawarar ɗauka.
Kwamishinan ya ce Ma’aikatar Ilimin Kimiyya da Fasaha za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da Ma’aikatar lafiya domin tabbatar da samar da ingantaccen lafiya ga masu malamai da dalibai.
Bisa wannan dalilin makarantu zasu koma ne Litinin, 28 ga Satumba, 2026.
Gwamnatin jihar ta yaba da fahimta da haɗin kan iyaye da malamai da masu makarantu da sarakunan gargajiya daƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi.
Fassara: Hauwa’u Mihammed Lawal
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
