Labarai
NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
Daga Aminu Dalhatu, Gusau
Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru 58, Emmanuel Okonkwo, bisa zargin yin safarar wiwi, tramadol, diazepam da sauran ƙwayoyin da doka ta hana.
An kama wanda ake zargin ne a ranar 10 ga watan Satumba, 2026, da misalin ƙarfe 11:30 na dare, a shagonsa da ke yankin Bakin Tasha, Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji ta jihar.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, ASCI Umar Mohammad, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wanda ake zargin tare da wasu waɗanda ake zargi da aikata laifuka a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya shafe sama da shekaru 20 yana gudanar da wani shagon sayar da magunguna a Birnin Magaji.
Ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa ya haɗa baki da wasu mutane biyu, waɗanda ake kira Yellow da Sadiq, waɗanda a yanzu haka suke tsere, wajen safarar ƙwayoyin maye masu haɗari.
Kayayyakin da aka ƙwato daga hannunsa sun haɗa da fakiti 112 na wiwi, allunan Exol 5 guda 1,160, sachet 14 na tramadol da allunan Diazepam D10 guda 133.
NSCDC ta ce an miƙa wanda ake zargin ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, domin ci gaba da gudanar da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.
A wani labarin kuma, rundunar ta kama wasu mutane tara bisa zargin haɗa baki wajen aikata laifi, lalata dukiyar jama’a, barna da kuma satar kayan rufin makaranta daga Makarantar Firamare ta Tsageru da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe.
Umar Mohammed ya bayyana cewa Sakataren Ilimi na Ƙaramar Hukumar Tsafe, Abdulrahman Aliyu, ne ya kai rahoton lamarin ga rundunar.
Rundunar ta ce an kama wanda ake zargi da jagorantar aikata laifin, Haruna Amadu, mai shekaru 55, ɗan ƙauyen Tsageru, a ranar 8 ga watan Satumba, 2026, da misalin ƙarfe 3 na rana. Daga nan ne bincike ya kai ga gano tare da kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a lamarin.
Ana zargin mutanen da haɗa baki wajen cire kayan rufin makarantar ba tare da izinin Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ba.
Rundunar ta ce waɗanda ake zargin sun kuma yi ƙoƙarin shawo kan hakiman gunduma da na ƙauye domin su ba su damar shiga harabar makarantar da kwashe kayan, amma shugabannin gargajiyar sun ƙi amincewa da buƙatarsu, tare da ba su shawarar su daina aikata hakan.
Fassara; Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoGwamnan Kano Ya Mika Sunayen Sabbin Kwamishinoni 2 Ga Majalisa Domin Tantancewa
-
Labarai5 days agoGwamnatin Neja Ta Jaddada Ƙudurinta Na Farfaɗo Da Kamfanin Buga Takardun Gwamnati
-
Labarai5 days agoAn Ceto Wani Mutum da Ya Fada Kududdufi a Kano
-
Labarai5 days agoTsangayar Kimiyyar Kula Da Lafiya Ta BUK Ta Lashe Zinare A Gasar Kwallon Ƙafa Ta Tsangayu Karo Na 19
-
Labarai3 days agoJigawa: Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Kafa Kwamitin Tantance Bayanan Maniyyatan 2027
-
Labarai5 days agoDan Takarar Gwamnan Sokoto Na ADC Ya Tsalleke Rijiya da Baya Daga Yunkurin Hallaka Shi
-
Labarai5 days agoShugaban Majalisar Wakilai Ya Jaddada Muhimmancin Samar Da Ilimi, Lafiya Da Tsaro Ga Al’umma
-
Labarai5 days agoDurumbun Gusau Ya Bukaci Haɗin Gwiwa Wajen Magance Matsalar Tsaro
