Labarai
Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
Daga KHADIJAH ALIYU, Kano
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin faɗaɗa tsarin ban-ruwa na Dam ɗin Watari da ke Ƙaramar Hukumar Bagwai.
Wannan ya biyo bayan muhawarar da aka gudanar a zauren majalisar yayin zaman ta na yau da kullum, wanda Kakakin Majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ya jagoranta.
Da yake gabatar da ƙudiri kan aikin ban-ruwan Dam ɗin Watari, ɗan Majalisar mai wakiltar mazaɓar Bagwai/Shanono, Ali Lawan Alhassan, ya ce an gina dam ɗin ne a shekarar 1988 domin bunƙasa kamun kifi, shawo kan ambaliyar ruwa, ban-ruwa da kuma samar da ruwan sha ga al’ummomin wasu sassan arewacin Kano.
Dan Majalisar ya bayyana cewa Bankin Raya Musulunci ya bayar da kwangilar faɗaɗa tsarin ban-ruwan a shekarar 2022, tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin shirin bunƙasa noma na jihar.
A cewarsa, an tsara aikin ne domin samar da damar yin ban-ruwa a kusan hekta 1,000 na gonaki, tare da bunƙasa harkokin noma tsakanin manoman yankin.
Sai dai Ali Lawan ya nuna damuwa kan yadda aka yi watsi da aikin, inda ya ce ɗan kwangilar ya bar wurin aikin.
Ya ce barin aikin ya haifar da buɗaɗɗun ramuka a gonaki, lamarin da ke jefa rayukan jama’a cikin haɗari tare da jefa mazauna al’ummomin da abin ya shafa cikin wahalhalu.
Saboda haka, ɗan Majalisar ya buƙaci Majalisar ta kafa kwamiti domin gudanar da cikakken bincike kan aikin, ciki har da yadda aka bayar da kwangilar, tare da gabatar da shawarwarin da suka dace domin ɗaukar matakin da ya kamata.
Ɗan Majalisar mai wakiltar mazaɓar Tudun Wada, Lawan Sule Shuwaki, ne ya mara wa ƙudirin baya.
A wani ci gaban makamancin haka, Majalisar ta kuma buƙaci gwamnatin Jihar Kano da ta gina magudanan ruwa domin samar da yanayi mafi aminci da dacewa ga mazauna garin Makera da ke mazabar Fagwalawa, Ƙaramar Hukumar Dambatta.
Ɗan Majalisar mai wakiltar mazaɓar Dambatta, Murtala Musa Kore, ne ya gabatar da ƙudirin.
Bayan doguwar muhawara, Majalisar ta amince da ƙudurorin biyu tare da yin kira ga gwamnatin jihar da ta ɗauki matakan da suka dace.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai7 days agoZa a yi makonni kafin tantance waɗanda gobarar jirgin ruwan Philippine ta shafa
