Labarai
INEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna
Daga Abdullahi Shettima
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), reshen jihar Kaduna, ta kaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwar Hukumomi kan Ilimantar da Masu Zaɓe da Wayar da Kan Al’umma (SICVEP), domin ƙarfafa ilimantar da masu zaɓe, wayar da kan jama’a da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Mukaddashin Kwamishinan Zaɓe na jihar, Malam Abba Yahaya, ne ya bayyana hakan yayin taron farko na kwamitin da aka gudanar a Kaduna.
Ya ce kwamitin zai samar da ingantaccen tsarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki, domin inganta ilimantar da masu zaɓe da ƙarfafa shigar jama’a cikin harkokin dimokuraɗiyya.
Malam Abba Yahaya ya ce kwamitin zai samar da tsare-tsare na matsakaici da dogon zango kan ilimantar da ‘yan ƙasa da masu zaɓe, tare da gano ƙungiyoyin da za su taimaka wajen gudanar da ayyukan da kuma bai wa hukumar shawarwari kan hanyoyin wayar da kan jama’a.
Ya ƙara da cewa kwamitin zai kuma mayar da hankali wajen rage ƙaurace wa zaɓe, inganta kyawawan halaye tsakanin al’umma da kuma dakile rikice-rikicen zaɓe da sauran maguɗan zaɓe.
Mukaddashin Kwamishinan Zaɓen ya sanar da cewa hukumar ta tsara gudanar da gwajin na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS da ɗora sakamakon zaɓe a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2026, domin tantance yadda na’urar za ta yi aiki a yanayi daban-daban.
Ya bayyana cewa an zaɓi rumfunan zaɓe biyu a kowace mazabar rajista, inda aka samu jimillar rumfunan zaɓe 510 a faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.
Dangane da aikin rajistar masu zaɓe, ya ce hukumar ta fara raba katunan zaɓe na dindindin (PVCs) ga waɗanda suka yi rajista a kashi na farko da na biyu tun ranar 9 ga Oktoba, 2026, yayin da ake jiran katunan waɗanda suka yi rajista a kashi na uku.
Ita ma shugabar sashen Ilimantar da Masu Zaɓe da Wayar da Kan Jama’a ta INEC a Kaduna, Hajiya Rukayya Sani Imam, ta ƙara haske kan manufofi da nauyin da ke bisa kwamitin haɗin gwiwar.
Ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki wajen kai saƙonnin ilimantar da masu zaɓe da wayar da kan jama’a zuwa sassa daban-daban na jihar.
Hajiya Rukayya ta kuma bayyana buƙatar ci gaba da wayar da kan jama’a domin ƙarfafa masu cancantar kaɗa ƙuri’a su shiga zaɓe, su guji tashin hankali tare da kiyaye ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
A nasa ɓangaren, Mukaddashin Kwamishinan Zaɓen ya buƙaci mambobin kwamitin da su gudanar da wannan aiki cikin kishin ƙasa da jajircewa, domin tabbatar da sahihin zaɓe mai gaskiya, haɗa kowa da kowa da zaman lafiya a jihar Kaduna.
Yusuf Zubairu
-
Labarai5 days agoJigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a
-
Labarai3 days agoNIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu
-
Labarai4 days agoGobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara
-
Labarai4 days agoShugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo
-
Labarai5 days agoZa a Gabatarda Zaben Kananan Hukumomi a 2027 a Kaduna
-
Labarai2 days agoAn Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki
