Labarai
Gobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Wata gobara da ta tashi da tsakar dare ta ƙona shaguna takwas da shagunan kwantena guda biyu a yankin Opomalu da ke Ƙaramar Hukumar Ilorin East ta Jihar Kwara.
Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Hassan Adekunle, ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa kan tashin gobarar a wani rukunin shaguna.
Ya bayyana cewa jami’an kashe gobarar sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka fara aikin kashe wutar domin hana ta bazuwa zuwa gine-ginen da ke maƙwabtaka da wurin.
Sanarwar ta ce gobarar ta shafi shaguna takwas da kwantena biyu, yayin da jami’an hukumar suka yi ƙoƙarin shawo kan lamarin da kuma rage asarar dukiyoyi.
Binciken farko ya nuna cewa wata matsalar wutar lantarki, wadda ta haddasa ƙarin ƙarfin lantarki, na iya zama sanadin tashin gobarar.
Babban Jami’in Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Alabi Muhammed, ya shawarci masu gidajen abinci da sauran masu sana’ar girki da ke amfani da gawayi ko itacen girki, da su tabbatar sun kashe wutar gaba ɗaya bayan kammala girki kafin barin wuraren sana’arsu.
-
Labarai5 days agoJigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a
-
Labarai3 days agoNIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu
-
Labarai4 days agoShugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo
-
Labarai1 day agoINEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna
-
Labarai5 days agoZa a Gabatarda Zaben Kananan Hukumomi a 2027 a Kaduna
-
Labarai2 days agoAn Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki
