Connect with us

Labarai

Jigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Mukaddashin Babban Alƙalin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a ta Jihar Jigawa, Umar Nasir Ahmad, ya fara ziyarar aiki a kotunan Shari’a da ke faɗin jihar, domin sanin halin da kotunan ke ciki da kuma ƙarfafa gwiwar ma’aikata wajen inganta ayyukansu.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Abbas Rufa’i Wangara ya bai wa  gidan Rediyon Najeriya a Dutse, ya bayyana cewa zuwa yanzu, ziyarar ta kai shi kotunan Shari’a da ke Kado-Wawa, Bulangu, Kafin-Hausa, Auyo da Hadejia.

A yayin ziyarar, Umar Nasir Ahmad ya jaddada aniyar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a, ta kula da walwala da bunƙasa ƙwarewar ma’aikatan kotuna.

Ya bayyana cewa ƙarfafa gwiwar ma’aikata na da muhimmanci wajen tabbatar da ingantaccen tsarin gudanar da shari’a.

Mukaddashin Babban Alƙalin ya buƙaci ma’aikatan da su kasance masu jajircewa, ladabi da riƙon amana w

ajen gudanar da ayyukansu, yana mai tunatar da su cewa bai kamata su ci amanar amincewar da al’umma ta yi musu ba.

Yayin ziyarar tasa ya samu rakiyar Magatakardar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a, Barrister Kabiru Abubakar Gumel; Babban Jami’in d je Kula da Kotunan Shari’a, Barrister Isma’il Sani; da  mataimakinsa na Shiyyar Hadejia, Barrister Isyak Mohd, da sauran manyan jami’an kotun.

Abbas Rufa’i Wangara ya ce ana sa ran za a ci gaba da ziyarar zuwa sauran kotunan Shari’a da ke faɗin jihar, inda Mukaddashin Babban Alƙalin ya tabbatar da cewa bayanan da za a tattara yayin ziyarar za su taimaka wajen jagorantar sauye-sauyen da ake gudanarwa domin ƙarfafa tsarin shari’a a Jihar Jigawa.

Fassara: Safiyah Abdulkadir

Labarai

Labarai1 day ago

INEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna

Daga Abdullahi Shettima Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), reshen jihar Kaduna, ta kaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwar...

Labarai2 days ago

An Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki

An bukaci masu aikin kula da lafiyar al’umma da su kasance masu bin ka’idojin sana’arsu tare da kiyaye martabar aikin,...

Labarai3 days ago

NIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo

Daga Usman Muhammad Zaria  Cibiyar Nazarin Kimiyyar Dabbobi ta Ƙasa (NIAS) ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da...

Labarai4 days ago

Gobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara

Daga Ali Muhammad Rabi’u  Wata gobara da ta tashi da tsakar dare ta ƙona shaguna takwas da shagunan kwantena guda...

Labarai4 days ago

Shugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo

Daga Khadijah Aliyu Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore, ya ƙaddamar da sabon ofishin ’yan sanda na shiyya...

Labarai5 days ago

Jigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a

Daga Usman Muhammad Zaria  Mukaddashin Babban Alƙalin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a ta Jihar Jigawa, Umar Nasir Ahmad, ya fara...

Labarai5 days ago

Za a Gabatarda Zaben Kananan Hukumomi a 2027 a Kaduna

Hukumar Zaɓe ta Jihar Kaduna (KADSIECOM) ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin jihar a...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu

Daga Sani Dutsinma  Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ta kammala shirye-shiryen tarbar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin halartar gangamin yaƙin...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 1 Don Bunƙasa Kiwo Da Sana’o’i

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe naira biliyan 1.124 domin ginawa da gyara cibiyoyin kiwo...

Labarai1 week ago

Tinubu Ya Gargadi ’Yan Siyasa Kan Tashin Hankali Gabanin Zaɓen 2027

Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan guje wa tashin hankali,...

Mafi Shahara