Connect with us

Labarai

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da ya dauka domin amfanin kasa, musamman cire tallafin man fetur da daidaita farashin canjin kudade.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar tawagar kungiyar PBAT Door-to-Door Movement, karkashin jagorancin shugaban kamfanin tsaro mai zaman kansa na Tantita Security Services Nigeria, Mista Kestin Ebimorbowei Pondi, a Dutse.

Tawagar ta je Jigawa ne domin kaddamar da reshen kamfanin a jihar, tare da gabatar da motocin yakin neman zabe guda 31 da za su taimaka wajen wayar da kan jama’a gabanin babban zaben 2027.

Namadi ya ce sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta aiwatar sun kara kudaden da gwamnatocin jihohi ke samu. A cewarsa, hakan ya taimaka wajen biyan albashi da fansho, da kuma aiwatar da ayyukan raya kasa.

Sai dai ya jaddada cewa ya kamata karin kudaden su haifar da sauye-sauye masu amfani ga jama’a, ciki har da samar da ayyukan yi, inganta samar da abinci, gina ababen more rayuwa da bude karin damammaki.

Gwamnan ya bayyana Tinubu a matsayin dan kishin kasa, a don haka ya bukaci tawagar ta kara tuntubar jama’a, domin mutane da dama ba su fahimci manufofi da nasarorin gwamnati yadda ya kamata ba.

 

Ya ce tattaunawa kai tsaye da masu zabe, da kuma sauraron matsalolinsu da bayyana ayyukan gwamnati na da muhimmanci wajen kara fahimta da goyon baya.

Namadi ya tuna da ziyarar da Tinubu ya kai Jigawa a baya-bayan nan, yana mai cewa kyakkyawar tarbar da jama’a suka yi masa ta nuna goyon bayansu ga shugabancinsa.

Ya tabbatar wa tawagar cewa gwamnatin jihar za ta ba kungiyar hadin kai domin samun nasarar Tinubu da sauran ‘yan takarar APC a zaben 2027.

A nasa bangaren, Pondi ya ce kungiyar za ta rika isar da manufofin gwamnati ga jama’a ta hanyar ziyartar gidaje da al’ummomi, tare da sauraron korafe-korafensu.

Ya bayyana cewa motocin 31 suna dauke da na’urorin magana, janareto, amsakuwa da makirufo. Ya kara da cewa kungiyar ta riga ta ziyarci kusan jihohi 23 a wani shirin wayar da kan jama’a na kasa baki daya.

Fassara: Safiyah Abdulkadir

Labarai

Labarai12 hours ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai15 hours ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai2 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai2 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai2 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai2 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai3 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai4 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai4 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Mafi Shahara