Labarai
Jigawa Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 1 Ga Ayyukan Samar Da Ruwa
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe naira biliyan 1.116 domin gudanar da ayyukan samar da ruwan sha a mazaɓu 23 na jihar, ƙarƙashin ayyukan mazabu na shekarar 2026 na Majalisar Dokokin jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar a gidan gwamnati da ke Dutse.
Ya ce an ware naira miliyan 907 domin ayyukan da Hukumar Samar da Ruwa da Tsaftar Muhalli ta Ƙauyuka (RUWASA) za ta aiwatar, yayin da Hukumar Samar da Ruwa a Ƙananan Garuruwa (STOWA) za ta gudanar da ayyukan da aka ware wa naira miliyan 208.5.
Ayyukan sun haɗa da haƙa rijiyoyin burtsatse masu amfani da injinan tuka- tuka, gina rijiyoyin samar da ruwa masu amfani da hasken rana, girka famfunan ruwa na ƙarƙashin ƙasa da na’urorin hasken rana, tare da gyara da inganta tsofaffin cibiyoyin samar da ruwa.
Kwamishinan ya bayyana cewa, an tsara ayyukan ne domin inganta samun tsaftataccen ruwan sha, musamman a ƙauyuka da sauran wuraren da ba su da isassun hanyoyin samar da ruwa.
Ya ƙara da cewa ayyukan za su taimaka wajen inganta lafiyar al’umma da tsaftar muhalli, rage dogaro da wutar lantarki da man fetur wajen samar da ruwa, tare da ƙarfafa amfani da makamashin hasken rana.
Sagir Musa Ahmed ya ce ana sa ran hukumomin da aka ɗora wa alhakin gudanar da ayyukan za su tabbatar da inganci, kulawa ta musamman, gaskiya da riƙon amana wajen aiwatar da su.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai5 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai6 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai6 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai6 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
-
Labarai3 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
