Labarai
Tsangayar Kimiyyar Kula Da Lafiya Ta BUK Ta Lashe Zinare A Gasar Kwallon Ƙafa Ta Tsangayu Karo Na 19
Daga Khadijah Aliy, Kano
Tsangayar Kimiyyar Lafiya ta Farko (Basic Medical Sciences) ta Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), ta doke Tsangayar Kimiyyar Zamantakewa (Social Sciences) da ci 5-3 a bugun fenariti, wato bugun da kai sai mai tsaron gida inda ta lashe lambar zinare ta gasar ƙwallon ƙafa a gasar wasannin tsangayu ta jami’ar karo na 19.
An tashi kunnen doki a lokacin da aka kammala mintuna 90 na wasan, lamarin da ya tilasta wa tsangayun biyu fafatawa a bugun fenariti domin tantance wadda za ta yi nasara.
Daraktan Wasanni na BUK, Farfesa Rabiu Mohammed, ya nuna godiyarsa ga Shugaban Jami’ar, Farfesa Haruna Musa, bisa cikakken goyon bayan da yake bayarwa, wanda ya taimaka wajen samun nasarar gudanar da gasar wasannin tsangayu ta 19.
Shugaban Kwamitin Ba da Shawarwari kan Wasanni, Farfesa Abdullahi Darki, ya ce gasar ta samar da dama ga ɗalibai da ma’aikatan jami’ar wajen haɗuwa da mu’amala da musayar ra’ayoyi.
Ya ƙara da cewa gasar ta kuma ba masu horas da ’yan wasa na jami’ar damar gano ƙwararrun ’yan wasa waɗanda za su iya wakiltar Jami’ar Bayero a gasannin wasanni na ƙasa da ƙasa.
Farfesa Darki ya buƙaci ɗaliban da ke fafatawa a wasanni da su yi amfani da wuraren wasanni da jami’ar ta samar domin haɓaka ƙwarewarsu da kuma baje kolin baiwarsu.
Ya jaddada cewa za a ci gaba da neman ƙwararrun ’yan wasa domin ƙarfafa wakilcin jami’ar a manyan gasannin wasanni.
Shi ma shugaban Tsangayar Basic Medical Sciences, Farfesa A. G. Alhassan, ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da tsangayarsa ta samu, yana mai cewa lashe lambar zinare a ƙwallon ƙafa babban abin alfahari ne.
Ya ce wannan ne karon farko tun bayan kafuwar tsangayar da ta samu nasarar lashe lambar zinare a gasar ƙwallon ƙafa.
Farfesa Alhassan ya taya ’yan wasan murna bisa jajircewarsu da ƙoƙarin da suka yi wajen tabbatar da nasarar tsangayarsu.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
-
Labarai19 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
