Labarai
An Ceto Wani Mutum da Ya Fada Kududdufi a Kano
Daga Khadijah Aliyu, Kano
Hukumar kashe gobara ta ceto wani mutum mai shekaru 42, mai suna Sani Uba Kwaru, bayan ya faɗa cikin wani kududdufi a yankin Ɗan Agundi da ke cikin birnin Kano.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Kabiru Isah Jafar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ciki har da jaridar TNL Hausa, ya bayyana cewa, sun samu kiran neman agaji da misalin ƙarfe 1:00 na rana, bayan faruwar lamarin.
Ya ce nan take jami’ansu suka garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka gudanar da aikin ceton, tare da nasarar fito da mutumin daga cikin ruwan.
Rahoton ya bayyana cewa bayan an ceto mutumin ya fito a some, yayin da jami’an suka yi nasarar fito da shi daga kududdufin.
Hukumar ta yi kira ga mazauna yankin da sauran al’umma da su riƙa taka-tsantsan, musamman a kusa da kududdufin da sauran wuraren da ka iya jefa rayuwarsu cikin haɗari.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
-
Labarai19 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
