Connect with us

Labarai

Gwamnatin Neja Ta Jaddada Ƙudurinta Na Farfaɗo Da Kamfanin Buga Takardun Gwamnati

Published

on

Daga Aliyu Lawal, Minna

Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da shirinta na inganta ayyuka da ƙwarewar gudanarwa a Kamfanin Buga Takardun Gwamnati (Government Printing Press), domin cimma manufofin da aka kafa kamfanin a kansu.

Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Abubakar Usman, ne ya bayar da wannan tabbacin yayin ziyarar aiki da ya kai kamfanin, wanda ke ƙarƙashin ofishinsa, domin duba ayyukan gyara da sabunta gine-ginensa da aka gudanar.

Yayin da yake jawabi ga ma’aikatan kamfanin, Alhaji Abubakar Usman ya buƙace su da su rungumi dabarun tallata ayyukan kamfanin ta hanyar jawo kwangilolin buga takardu daga hukumomin gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran waɗanda za su iya amfani da ayyukansa.

Sai dai ya ba da shawarar cewa ma’aikatan da suka samar da kwangilolin buga takardu daga wajen kamfanin su riƙa samun wani kaso na kuɗin da aka samu daga waɗannan ayyuka, a matsayin wani nau’in ƙarfafa musu gwiwa domin haɓaka ƙwazo, tabbatar da ɗorewar kamfanin da kuma zaburar da su wajen bayar da gudummawa ga ci gabansa.

Sakataren Gwamnatin ya jaddada cewa nasarar kamfanin za ta dogara ne musamman kan jajircewa, sadaukarwa da haɗin gwiwar ma’aikatansa, inda ya buƙace su da su nuna ƙwarewa da cikakken nauyin da ke kansu wajen gudanar da ayyukansu.

Tun da farko, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Siyasa, ESV James Bake, wanda kuma ke kula da Sashen Ayyuka na Musamman, ya bayyana cewa an samu damar gyara gine-ginen kamfanin ne sakamakon amincewar da aka bayar na amfani da kuɗaɗen da aka samu daga ayyukan buga takardu da aka gudanar wa hukumomin gwamnati.

Ya ƙara da cewa tun bayan fara kula da Sashen Ayyuka na Musamman, ya ƙaddamar da wasu matakai da nufin farfaɗo da kamfanin buga takardun gwamnati mallakar jihar, tare da dawo da ƙarfinsa wajen samar da ingantattun ayyukan buga takardu masu aminci da kuma gogayya da sauran kamfanoni.

Fassara: Shafii Abubakar Wababe

Labarai

Labarai19 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai1 day ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai1 day ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai1 day ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai1 day ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai2 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara