Kasuwanci
APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari
Daga SANI DUTSINMA
Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce Jihar Kebbi na goyon bayan ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a babban zaɓen shekarar 2027.
Sanata Yari ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai jihar Kebbi, inda ya gana da Gwamna Nasir Idris, sarakunan gargajiya da sauran shugabannin jam’iyyar a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
Ya yaba wa gwamnan da sauran shugabannin APC bisa ƙoƙarin da suke yi wajen tattara goyon bayan jama’a ga jam’iyyar, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa haɗin kansu zai taimaka wajen samun nasara ga Tinubu da sauran ’yan takarar APC a zaɓen 2027.
Yari ya ce kwamitin yaƙin neman zaɓen zai yi aiki tare da dukkan mutane da ƙungiyoyin da suka himmatu wajen goyon bayan sake zaɓen Tinubu, ba tare da la’akari da matsayinsu ba, domin cimma manufofin jam’iyyar.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa kan goyon bayan da APC ke samu a Kebbi, bisa abin da ya gani yayin ziyarar da ya kai jihar.
Daraktan yaƙin neman zaɓen ya amince da cewa ƙasar na fuskantar ƙalubale, amma ya ce gwamnatin Tinubu tana ƙoƙarin shawo kansu. Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi tunani kan dangantakarsu da Allah, yana mai cewa yaƙi da rashin tsaro na buƙatar haɗin kan kowa da kowa.
A nasa jawabin, Gwamna Nasir Idris ya bayyana ziyarar tawagar kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a matsayin abin farin ciki, yana mai cewa ya ji daɗin yadda shugabannin APC da sarakunan gargajiya suka taru domin tarbar tawagar.
Ya ƙara da cewa sarakunan sun yanke shawarar haɗuwa a fadar domin nuna goyon bayansu da kuma maraba da tawagar.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
