Labarai
Gwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
Daga Usman Sani, Kaduna
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana bunƙasa ƙwarewar matasa a sana’o’i a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen farfaɗo da tattalin arziki da haɗa kowa cikin ci gaban al’umma a Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen bikin aza harsashin ginin Cibiyar Bunƙasa Ƙwarewa ta Hukumar NASENI da aka gudanar a Rigachikun, Ƙaramar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
Uba Sani ya ce matasan Najeriya na da kuzari, buri da basirar da za su amfana da shirye-shiryen koyon sana’o’i, don haka ya zama wajibi gwamnati ta samar musu da ingantattun hanyoyin da za su cimma burinsu.
Ya tuna cewa a watan Agustan wannan shekara, matasa 4,050 ne suka kammala karatu a cibiyoyin bunƙasa ƙwarewa guda uku na gwamnatin jihar da ke Rigachikun, Soba da Samaru Kataf, inda suka koyar da sana’o’i guda 14.
A cewarsa, kafa cibiyar NASENI wani jari ne a fannin ilimi, ƙwarewa da kasuwanci, wanda zai taimaka wa mutane su samu hanyoyin dogaro da kai da ingantacciyar rayuwa, tare da samar da ɗorewar wadata ga al’umma.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na fatan cibiyar za ta samar da shirye-shiryen koyarwa da suka ginu kan ƙwarewar aikace-aikace, takardun shaidar kammala karatu masu inganci da kuma hanyoyin samun aikin yi ko kafa sana’o’in dogaro da kai.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
