Labarai
NMA Ta Yi Alƙawarin Inganta Tsaron Lafiya Da Jin Daɗin Likitoci
Daga KHADIJAH ALIYU
Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta yi alƙawarin ci gaba da fafutukar ganin an samar da tsarin kiwon lafiya da ke tabbatar da tsaro da ingancin aikin likitoci, samar da ingantaccen kulawa ga marasa lafiya da kuma kyakkyawar makoma ga matasan likitoci a ƙasar.
Shugabar reshen ƙungiyar ta jihar Kano, Dakta Abubakar Nagoma Usman, ce ta bayyana hakan yayin da take yi wa manema labarai bayani kan shirye-shiryen bikin Makon Likitoci na bana, mai taken “Tabbatar Da Makomar Aikin Likitanci A Najeriya”, a Kano.
Usman ta ce ƙungiyar ta ci gaba da jajircewa wajen bayar da shawarwari na ƙwararru, inganta bin ƙa’idojin aikin likitanci, tallafa wa ci gaba da koyon sana’ar likitanci da kuma fafutukar samar da manufofin da za su inganta jin daɗin likitoci da kula da marasa lafiya.
Ta buƙaci al’umma da su ba da muhimmanci ga rigakafin cututtuka ta hanyar zuwa duba lafiyarsu akai-akai, yin gwaje-gwajen da suka dace, neman kulawar likita da wuri da kuma karɓar shawarwarin lafiya daga ƙwararrun ma’aikatan lafiya.
Shugabar NMA ta kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su haɗa kai da ƙungiyar likitoci wajen yaɗa sahihan bayanan lafiya, yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya, ƙarfafa rayuwa mai kyau da kuma wayar da kan jama’a game da jin daɗin likitoci da buƙatar zamanantar da tsarin samar da kiwon lafiya.
Usman ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta ayyukan kiwon lafiya a faɗin jihar.
Ta ce yabon ya samo asali ne daga matakan da gwamnatin ta ɗauka wajen inganta kayayyakin more rayuwa na kiwon lafiya, cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko, ayyukan agajin gaggawa, kula da cututtuka na musamman, bunƙasa ma’aikatan lafiya da samar da muhimman magunguna da kayan aikin likitanci.
Shugabar ta bayyana shirye-shiryen ƙungiyar na haɗa kai da gwamnatin jihar domin cimma manufofinta na kiwon lafiya da magance ƙalubalen da likitoci da ɓangaren kiwon lafiya ke fuskanta.
Ta kuma yi kira da a ci gaba da yin gyare-gyare a fannin koyar da likitanci domin shirya likitocin nan gaba don tunkarar buƙatun aikin likitanci na zamani.
A cewarta, ya kamata horar da likitoci ya ƙara mayar da hankali kan ƙwarewar amfani da fasahar zamani, sababbin dabarun fasaha, bincike da ci gaba da neman ilimi, domin samar wa likitoci ilimi da ƙwarewar da za su ba su damar bayar da ingantaccen kulawar lafiya.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
