Labarai
Jami’ar Ilorin Za Ta Yaye Ɗalibai Fiye da Dubu 16
Daga ALI MUHAMMAD RABIU
Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara, za ta yaye ɗalibai 16,152, inda 365 daga cikinsu suka samu digiri mafi daraja (First Class) a zangon karatu na shekarar 2025/2026.
Mataimakin Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Egbewole, SAN, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai kan bikin yaye ɗalibai karo na 41 na jami’ar, mai taken “Daga Tasiri Zuwa Gadon Da Za A Bari”, wanda aka gudanar a babban ɗakin taron jami’ar da ke Ilorin.
Ya ce cikin ɗaliban da za a yaye, 11,213 sun kammala karatun digiri na farko, yayin da 4,939 suka kammala karatun digiri na gaba da difloma. Ya bayyana cewa wannan na nuna ci gaba da mayar da hankali da jami’ar ke yi wajen inganta ilimi, horar da ƙwararru, bincike da kirkire-kirkire.
Farfesa Egbewole ya ce jami’ar na alfahari da nasarorin ɗaliban, yana mai cewa hakan ya samo asali ne daga ƙoƙarin ɗalibai, malaman jami’a, sauran ma’aikata, iyaye, masu kula da ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya bayyana cewa daga cikin ɗalibai 11,213 da suka kammala digiri na farko, 4,367 sun samu digiri na matakin aji na biyu (Second Class Upper), yayin da 5,102 suka samu aji na biyu na ƙasa (Second Class Lower). Haka kuma, ɗalibai 1,006 sun samu digiri na aji na uku, yayin da 30 suka kammala da takardar shaidar cin jarabawa (Pass).
Ya ce bikin zai kuma haɗa da ɗaliban da suka kammala kwasa-kwasan ƙwararru, ciki har da 19 da suka kammala Karatun Likitanci da Tiyata, 89 na jinya, 73 na harhaɗa magunguna, 41 na kula da lafiyar ido, 89 na gyaran jiki da kuma 32 na likitancin dabbobi.
Mataimakin shugaban jami’ar ya ce a matakin karatun gaba da digiri na farko, jami’ar za ta bayar da difloma ta gaba da digiri ga mutum 160, digiri na biyu ga 901, digiri na biyu na ƙwararru ga 114, da kuma digirin digirgir (PhD) ga mutum 251. Bugu da ƙari, ɗalibai 3,511 za su kammala karatu ta Cibiyar Jami’ar Mai Kula da Cibiyoyin da ke Ƙarƙashinta.
Ya ce mahukuntan jami’ar sun inganta harkokin fasahar zamani da sauran fannoni na ci gaba.
Farfesa Egbewole ya bayyana cewa wannan yunƙuri ya taimaka wajen inganta jami’ar tare da tafiya daidai da manufar kafa ta.
Ya ce bikin na nuna jajircewar jami’ar wajen ci gaba, tun daga tabbatar da ingancin karatu zuwa mayar da harkokinta na zamani ta hanyar amfani da fasahar dijital, yana mai cewa ana fatan ƙara ƙarfafa tsarin domin samun ci gaba fiye da yadda ake tsammani.
Shugaban shugaban jami’ar ya ƙara da cewa an ba da fifiko ga jin daɗin ma’aikata da ɗalibai domin inganta rayuwarsu.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
