Fasaha
Jigawa Ta Amince Da Kwangilolin Sama Da Naira Biliyan 1.3
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da bayar da kwangilolin da darajarsu ta haura naira biliyan 1.3, domin ingantawa da faɗaɗa kayayyakin aiki a kafafen yaɗa labarai a jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya ce kwangilolin sun haɗa da girka na’urar watsa shirye-shirye ta Harris Digital AM mai ƙarfin 50KW ga gidan rediyon Jigawa, da kuma na’urorin FM masu ƙarfin 3KW guda biyar.
Ya ce, za a kuma gina kananan tashoshin FM guda biyar a ƙananan hukumomin Gumel, Gwaram, Hadejia, Kazaure da Ringim.
Kwamishinan ya ce ayyukan za su taimaka wajen faɗaɗa samun tashoshin rediyo tare da inganta watsa shirye-shirye ta hanyar amfani da na’urar zamani.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ƙara da cewa Majalisar Zartarwar jihar ta kuma amince da Ma’aikatar Lafiya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Malaria Consortium ƙarƙashin shirin SARMAAN II, da tallafin Gidauniyar Bill & Melinda Gates.
Ya ce haɗin gwiwar na tsawon shekaru huɗu zai taimaka wajen rage cutar zazzabin cizon sauro ta hanyar ba da tallafin fasaha, inganta amfani da bayanai da ƙarfafa samar da matakan kariya da maganin cutar ga al’umma da cibiyoyin lafiya.
Fassara : Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
