Labarai
Sanata Yari Ya Bada Gudummawar Kudi Ga Wadanda Harin Sama Ya Shafa A Maradun
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’azeez Yari Abubakar, ya bayar da naira miliyan 23 da kuma buhuna 105 na kayan abinci ga wadanda lamarin harin sama da Rundunar Sojin Sama ta kasa ta kai a Karamar Hukumar Maradun, Jihar Zamfara ya shafa.
A cikin wata sanarwa da aka fitar wa manema labarai, Shugaban Kwamitin sadarwa na kungiyoyin siyasar tsohon gwamnan, Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa an bayar da wannan gudummawar ne a lokacin ziyarar ta’aziyya da aka kai ga Mai Martaba Sarkin Maradun, Alhaji Garba Muhammad Tambari, a fadarsa.
Alhaji Abdul’azeez Yari Abubakar, wanda shi ne Sanatan da ke wakiltar yankin Zamfara ta yamma a Majalisar Dattawa ta kasa, an wakilce shi ne ta hannun Kwamishinan Tarayya a Hukumar Kidaya ta Kasa a Jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Muttaƙa Rini. Ya bayyana lamarin a matsayin nufin Allah.
Ya bukaci iyalan wadanda suka rasu da wadanda suka samu raunuka su dauki wannan lamarin a matsayin kaddara wanda ba zai yiwu a kauce masa ba.
Sanatan ya bayyana cewa, daga cikin shirye-shiryen agajin, kowanne iyali na wadanda suka rasu zai samu naira miliyan daya da buhuna biyar na abinci, yayin da wadanda suka ji rauni za su samu naira dubu dari biyar da buhuna biyu na abinci kowanne.
“Ya roki Allah SWT yai ma mutanen 13 da suka rasu sakamako da Aljannatul Firdausi, ya ba iyalansu da yankin Gidan Goga da Masarautar Maradun karfin hali don daukar wannan rashin da kuma saurin samun sauki ga wadanda suka ji rauni 20,” a cewar sanarwar.
Alhaji Abdul’azeez Yari Abubakar ya tabbatar wa da al’ummar Jihar Zamfara da dukkan yankin Arewa maso Yamma cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da niyyar dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jihar da kuma yankin baki daya.
A nasa bangaren, Mai Martaba Sarkin Maradun, Alhaji Garba Muhammad Tambari, ya yi godiya ga kyautar Sanatan, yana mai jaddada cewa wannan tallafin zai taimaka sosai wajen rage wahalar da wadanda abin ya shafa.
Sarkin ya bayyana matakin Sanata Abdulazeez Yari Abubakar a matsayin shaidar nuna martani mai kyau ga bukatun al’ummarsa a kowane lokaci.
Idan za a tuna, mafi yawan wadanda wannan mummunan lamari ya shafa sun fito ne daga kauyen Kakindawa na Karamar Hukumar Gidan Goga a Masarautar Maradun, Jihar Zamfara.
REL/AMINU DALHATU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
