Labarai
Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari
Daga Usman Muhammad Zaria
Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce yankin Arewa zai saka wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da dimbin ƙuri’u a zaɓen shekarar 2027.
Yari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayan APC a wajen gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a filin wasa na Dutse Township da ke Jihar Jigawa.

Ya ce Arewa ba ta manta da irin goyon bayan siyasa da gudunmawar da Tinubu ya bayar ga shugabannin yankin a baya ba, yana mai cewa yankin zai rama wannan alheri a lokacin zaɓe.
A cewarsa, sabanin wasu da ke ikirarin su ne ’yan Arewa na asali ba tare da wani abin a zo a gani da suka yi wa yankin ba, Tinubu ya kasance yana mara wa ’yan siyasar Arewa baya ta fuskar siyasa da ci gaba.
Ya ce Tinubu ya shafe shekaru yana tallafa wa shugabannin siyasa ba tare da son kai ba, har suka samu damar zama shugabannin ƙasa da kuma sake lashe zaɓe karo na biyu.

Daraktan yaƙin neman zaɓen ya bayyana fatan Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka wa Tinubu bisa irin jajircewarsa wajen yi wa ƙasa hidima, tare da ba su nasara a wannan tafiya ta siyasa.
Abdulaziz Yari ya bayyana dimbin mutanen da suka halarci gangamin Dutse a matsayin shaida ta goyon bayan da Tinubu ke samu a Arewa, yana mai cewa yankin ya haɗa kai kuma a shirye yake ya ba Shugaban ƙasar ƙuri’u masu yawa a zaɓen 2027.
Ya buƙaci masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su ci gaba da ƙarfafa gangamin neman goyon baya, domin tabbatar da gagarumar nasara ga APC.

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara ya kuma ba da labarin wata ganawa da ya yi da Tinubu a Saudiyya, inda ya nemi Shugaban ƙasar ya yi masa addu’a tare da yi wa daukacin tawagar yaƙin neman zaɓen addu’ar samun nasara.
A cewar Yari, Tinubu ya tabbatar masa da cewa za su yi nasara, yana mai bayyana ƙwarin gwiwarsa ga taimakon Allah a lokacin da suke gudanar da addu’o’insu.
Ya ce imanin Shugaban ƙasar, haɗe da gagarumin goyon bayan da yake samu a faɗin Arewa, ya ƙara masa ƙwarin gwiwar cewa APC za ta yi nasara a zaɓen 2027.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
-
Labarai19 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
