Connect with us

Labarai

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Published

on


Daga Usman Muhammad Zaria 

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu dauki domin magance matsalar zaizayar ƙasa, dawo da zirga-zirgar jiragen ƙasa a layin Kano zuwa Nguru, tare da sake duba harajin shigo da alkama da shinkafa domin kare manoman cikin gida.

Namadi ya yi wannan kiran ne yayin ziyarar aiki da Shugaba Tinubu ya kai Jihar Jigawa, inda ya ƙaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta gudanar tare da halartar gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a filin wasa na Dutse Township.

 

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ba za ta iya magance matsalar zaizayar ƙasa a wasu yankuna ita kadai ba, duk kuwa da ƙoƙarin da take yi.

Ya bayyana Hadejia, Dutse, Birnin Kudu da Gwaram a matsayin wasu daga cikin wuraren da matsalar ta fi kamari, waɗanda ke buƙatar  taimakon gwamnatin tarayya cikin gaggawa.

Namadi ya kuma buƙaci a dawo da dakon kaya a tsohon layin dogo na Kano zuwa Nguru, yana mai cewa hanyar na da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin jihohin Kano, Jigawa da Yobe.

A fannin noma, gwamnan ya buƙaci gwamnatin tarayya ta sake duba manufofin harajin shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje, musamman alkama da shinkafa, domin ƙarfafa noman cikin gida da kuma kare manoma daga asara.

Gwamnan ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa tallafa wa ayyukan ci gaba a Jigawa, musamman aikin samar da ruwan sha na Greater Dutse, wanda ya ce an kammala sama da kashi 60 cikin 100 na aikin.

Ya kuma amince da irin tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa a fannonin noma, ilimi, ababen more rayuwa da tallafin jin ƙai, inda ya bayyana cewa iyalai 192,000 a jihar sun amfana da shirin tallafin kuɗi na gwamnatin tarayya, wanda aka kashe Naira biliyan 14.36 daga shekarar 2024 zuwa lokacin jawabin.

Sauran ayyukan gwamnatin tarayya da ya ambata sun haɗa da aikin layin dogo na Kano zuwa Katsina zuwa Maradi, manyan hanyoyin tarayya na Gaya–Shuwarin–Azare da Kano zuwa Gumel zuwa Hadejia, da kuma kafa Kwalejin Noma ta Tarayya a Kirikasamma da Kwalejin Ilimi ta Tarayya a Birniwa.

 

Tun da farko, Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da Cibiyar Ƙera Kayayyakin Fasaha ta Renewed Hope, Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Bola Ahmed Tinubu da kuma hanyar Garu da aka faɗaɗa tare da gina titin biyu.

Gwamnatin jihar ta kuma ƙaddamar da taraktoci 400 da sauran kayan aikin noma domin ƙarfafa samar da amfanin gona.

Namadi ya jaddada goyon bayan gwamnatin jihar ga manufofin ci gaban gwamnatin tarayya, yana mai fatan cewa ci gaba da haɗin gwiwa zai taimaka wajen hanzarta ci gaban Jigawa da Najeriya baki ɗaya.

Fassara: Safiyah Abdulkadir 

Labarai

Labarai19 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai1 day ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai1 day ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai1 day ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai1 day ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai2 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara