Labarai
Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
Daga Isma’il Adamu
Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a hukumance.
Takardar murabus ɗin tasa, mai ɗauke da kwanan watan 2 ga Nuwamba, 2026, an aika ta ne zuwa ga Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina.
Kwararren ɗan jaridar, wanda ya ce ya yi murabus ne saboda wasu dalilai na kansa, ya gode wa Gwamna Dikko Umar Radda bisa amincewar da ya yi da shi domin yi wa jihar hidima a wannan matsayi cikin shekaru uku da suka gabata.
A cikin takardar, Zayyan ya ce murabus ɗin nasa zai fara aiki ne daga ranar 16 ga Nuwamba, 2026.
Ya bayyana cewa bayan shafe shekaru uku yana aiki a matsayin Babban Manajan KTTV, tun daga Nuwamba 2023 zuwa yanzu, ya yanke shawarar ajiye muƙamin domin wasu dalilai na kansa da kuma neman wasu damarmaki.
Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina ya karɓi takardar a ranar 6 ga Nuwamba, 2026.
Sai dai a wani rahoto na daban, an fitar da sanarwa ga manema labarai da ke bayyana cewa an sauke Abba Zayyan daga muƙaminsa, wadda aka sanya wa hannu a ranar 10 ga Nuwamba, kwanaki huɗu bayan ofishin Sakataren Gwamnatin jihar ya karɓi takardar murabus ɗinsa.
Abba Zayyan ya samu nasarori a harkar yaɗa labarai, inda ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Gidajen Rediyon Tarayya Kaduna (FRCN), Daraktan Sashen Watsa Shirye-shirye Kai Tsaye a Hedikwatar FRCN da ke Abuja, da kuma Babban Daraktan Hukumar Yaɗa Labarai ta Jihar Kaduna (KSMC).
Ya kuma riƙe wasu muhimman muƙamai a fannonin kafafen yaɗa labarai, hulɗa da jama’a da gudanarwa.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
-
Labarai19 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
