Connect with us

Labarai

Hukumar Alhazai Ta Jigawa Ta yi Tanadin Abinci na Musamman ga Masu Lalura

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa za ta ci gaba da samar da  abinci da musamman  ga Alhazan jihar da ke da matsalar hawan jini da ciwon sukari a yayin aikin Hajjin shekarar 2026.

Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci cibiyar gwajin lafiya a Asibitin Gwamnati na Dutse, babban birnin jihar.

 

A cewarsa, hukumar ta dade tana samar da wannan abinci na musamman ga Alhazan jihar a matsayin wani mataki na inganta lafiya da walwalar su.

Ya kara da cewa, hukumar na bai wa lafiya da walwalar kowanne Alhaji muhimmanci sosai, tare da bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen cimma burin da aka sanya a gaba.

 

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa, an kuma tsara shirin bayar da abinci sau uku ga Alhazan jihar a kasar Saudiyya.

A yayin da yake yin sharhi kan gwajin lafiya, shugaban hukumar ya ce mataki na hudu na gwajin yana tafiya cikin nasara bisa yadda Maniyyatan ke bada hadin kai.

Saboda haka, ya jaddada cewa hukumar ta himmatu himma wajen daukar nauyin kudaden gwajin lafiya, wanda kyauta ne ga dukkan Maniyyatan jihar.

Haka kuma, jagoran ƙungiyar likitoci, Dr. Abubakar Habib, ya tabbatar da kudurinsu na gudanar da gwajin lafiya bisa ka’idojin hukumar kula da Alhazan jihar da kuma hukumomin Hajj da Umrah na Saudiyya.

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara