Labarai
Hukumar Raya Kogin Benuwe Ta Bullo da Sabuwar Fasahar Kare Hanyar Ban-ruwa a Tafkin Geriyo
Daga Yusuf Zubairu/Abubakar Hamza
Shugaban Hukumar Raya Kogin Benuwe Dakta Mahmud Sanusi Mohammed, ya bullo da wata fasaha mai sauki da za ta kare hanyar shiga aikin ban-ruwa na Tafkin Geriyo daga zaizayewa a lokacin damina.
Wannan shiri ya biyo bayan ziyarar duba aikin samar da ruwa ga gonaki da ya kai, inda ya tantance matsalolin da ke haddasa zaftarewar hanyoyi musamman hanyar da ake wannan aiki.

A tsakiya, Shugaban Hukumar Raya Kogin Benuwe ne Dakta Mahmud Sanusi Mohammed
Domin magance matsalar, hukumar na amfani da wata sabuwar hanya wadda ta haɗa da amfani da tsofaffin tayoyin motoci da aka cika da dakakken dutse da tsakuwa. Ana jera tayoyin ne ta yadda za su matse juna, su zama wani gini mai ƙarfi domin hana zaizayar ƙasa da kuma daidaita magudanar ruwa.
An tsara wannan dabara ce domin rage ƙarfin ruwan da ke gudana a saman ƙasa, ƙarfafa ƙasa, da kuma hana zaftarewar hanya a lokacin damina.

Jami’ai sun bayyana cewa wannan hanya da aka bullo da ita tana da amfani matuka ga muhalli, domin tana ƙarfafa sake amfani da kayayyakin shara, tare da rage kuɗaɗen da ake kashewa wajen yin gyara.

Haka kuma ana sa ran wannan tsari zai ƙara ingancin hanyar shiga wurin tare da tabbatar da samun damar zuwa wuraren ban-ruwa a kowane lokaci na shekara.

Shugaban Hukumar ya shaidawa Rediyon Najeriya cewa,halin yanzu wannan aiki a cigaba da gudana, wanda ke nuna ƙudurin shugabancin hukumar na samar da mafita da za ta kare muhimman kayayyakin more rayuwa, tare da ƙarfafa ayyukan ban-ruwa masu dorewa a yankin.
-
Labarai6 days agoRamadan: Sarkin Kauru Ya Bukaci a Kara Karfafa Tsaro Tare da Tallafawa Marasa Galihu
-
Labarai5 days agoKaramar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
-
Labarai5 days agoSojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kano Ta Fara Shari’ar Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam
-
Labarai2 days agoRanar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata
-
Labarai5 days agoTsarin Kundin Shirin Bunkasa Samarda Abinci Mai Gina Jiki
-
Labarai6 days agoKungiyoyin Alumma a Jigawa Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Gwamna Namadi Kan Lamarin Walida Abdulhadi
-
Labarai4 days agoGwamnatin Zamfara Ta Ayana Dokar Ta-baci Kan Shan-Inna a Karamar Hukumar Gummi
