Connect with us

Labarai

Gwamna Namadi Ya Taya Najeriya Murnar Ranar Dimokuraɗiyya

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya taya al’ummar Najeriya da mazauna jihar murnar Ranar Dimokuraɗiyya ta shekarar 2026.

A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaransa, Hamisu Mohammed Gumel ya fitar, gwamnan ya bayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin muhimmiyar rana a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Ya ce ranar tana tunatar da sadaukarwar jaruman da suka yi gwagwarmaya domin tabbatar da adalci, ‘yanci da kuma haƙƙin jama’a na zaɓen shugabanninsu.

Gwamna Namadi ya bayyana cewa ranar na ba da damar yin nazari kan tafiyar dimokuraɗiyyar ƙasa da irin ci gaban da aka samu tsawon shekaru.

Ya jaddada cewa dimokuraɗiyya ba zaɓe kawai ba ce, har ila yau tana nufin gina cibiyoyi masu ƙarfi, kare haƙƙin jama’a da tabbatar da gaskiya da rikon amana a shugabanci.

Ya ce duk da ƙalubalen da Najeriya ta fuskanta, ƙasar ta ci gaba da samun ci gaba ta hanyar bin tsarin mulki da jajircewar al’umma.

Da yake magana kan Jigawa, Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta ci gaba da aiwatar da ajandarta 12 domin inganta ilimi, lafiya, noma, tattalin arziki da ababen more rayuwa.

Ya ƙara da cewa cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatin ta mayar da hankali wajen samar da damammaki ga jama’a da kuma tallafa wa marasa galihu a faɗin jihar.

Gwamnan ya yabawa sarakuna, malamai, jami’an tsaro da ƙungiyoyin al’umma bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a Jigawa.

A ƙarshe, ya yi kira ga jama’a su ci gaba da kasamcewa masu haƙuri, mutunta ra’ayoyin juna da shiga ayyukan raya ƙasa, tare da sake bayyana goyon bayansa ga ajandar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara