Labarai
PDP Ta Amince Da Ombugadu A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Nasarawa Na 2027
Daga Aliyu Muraki
Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa ta ayyana Dakta Emmanuel Ombugadu a matsayin ɗan takararta na gwamna a zaɓen 2027.
Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, Abdulmaleek Danga, ya bayyana hakan a Lafia, yana mai cewa Ombugadu ya samu tikitin ne ta hanyar maslaha.
Ya ce tsarin ya kasance cikin lumana, gaskiya da adalci, tare da yabawa mambobi da masu ruwa da tsaki bisa nuna haɗin kai da jajircewa.
A jawabinsa, Dakta Ombugadu ya gode wa mambobi da shugabannin jam’iyyar bisa amincewa da shi, tare da fatan samun nasara.
Ya kuma sake gabatar da abokin takararsa na 2023, Yahaya Ohinoyi, a matsayin mataimakinsa na zaɓen 2027, tare da kira ga magoya bayan PDP su ci gaba da haɗin kai domin samun nasara a babban zaɓen mai zuwa.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
