Labarai
Sanata Yari Ya Raba Shanu 500 a Zamfara
Daga Aminu Dalhatu
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanatan da ke wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari Abubakar, ya bai wa mambobin jam’iyyar APC a jihar shanu 500.
An raba shanun a fadin gundumomin siyasa 147 na jihar, inda kowace gunduma za ta sami shanu 3.

A cewar Dr. Lawal M. Liman, Gabdon Kaura, wannan tallafi al’ada ce ta shekara-shekara da ke da nufin tallafa wa shugabanni da mambobin jam’iyyar a lokutan bukukuwa.
Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai, Ibrahim Mohammed, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce an yi wannan tallafi ne domin bai wa mambobin jam’iyyar damar gudanar da bukukuwan Eid-el-Kabir cikin sauƙi.

Gabdo ya kuma buƙaci su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i ga ƙasar da shugabanninta, musamman Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya ce yana buƙatar addu’o’i fiye da kowane lokaci.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
