Ilimi
Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
Daga Aminu Dalhatu
Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar 2026, da nufin mayar da yara 453,602 da ba sa zuwa makaranta cikin tsarin ilimi.
Shugaban hukumar, Farfesa Nasir Garba Anka, ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin a Gusau, inda ya ce matsalar yara da ba sa zuwa makaranta ta shafi ƙasa baki ɗaya, kuma tana buƙatar haɗin gwiwar gwamnati, iyaye da al’umma.
Ya ce wani aikin rajista da tantance wuraren da yaran suke, wanda UNICEF ta tallafa, ya gano yara 453,602 a hukumomin kula da ilimi na ƙananan hukumomi 14 na jihar tsakanin shekarar 2024 da 2025.
Farfesa Anka ya bayyana cewa yara 432,319, wato kashi 95.3 cikin 100, suna yankunan karkara, yayin da 21,283, wato kashi 4.7, suke birane.


Ya ce yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne mayar da bayanan da aka tattara zuwa aiki, ta hanyar shigar da yaran makaranta, tabbatar da ci gaba da zuwa makaranta da kuma samun ingantaccen ilimi.
A nasa saƙon fatan alheru, jami’in dake kula da UBEC a Zamfara, Malam Tanimu Abdulkadir, ya yi kira ga iyaye, sarakunan gargajiya da malaman addini da su goyi bayan shirin, yana mai cewa dokar Ilimin Bai-daya ta tanadi ilimi kyauta kuma wajibi ga kowane ɗan Najeriya.


Ita ma memba ta uku ta ZSUBEB kuma jami’ar da ke kula da ayyukan UNICEF a jihar, Farfesa Rabiatu Musa Talata Mafara, ta buƙaci ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, UNICEF, UBEC, iyaye da al’umma, domin tabbatar da cewa dukkan yaran da aka gano sun samu damar zuwa makaranta.

Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
