Labarai
Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
Daga Sani Dutsinma
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin jinya da ake yi kyauta, wanda zai tallafa wa marasa lafiya dubu 1,500 a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi tawagar likitocin WAMY da suka kai masa ziyarar ban-girma a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Birnin Kebbi.

Ya ce aikin jinyar wani muhimmin tallafin jin ƙai ne da zai taimaka wajen inganta lafiyar al’ummar jihar, musamman mutanen da ba su da damar biyan kuɗin samun kulawar lafiya ta musamman.
Gwamna Nasir Idris ya gode wa WAMY da Gidauniyar Nasara bisa zaɓar Jihar Kebbi domin gudanar da shirin. Ya tabbatar wa tawagar cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da samar da yanayin da zai ba da damar gudanar da ayyukan jin ƙai da na kiwon lafiya.
Tun da farko, Daraktan Gudanarwa na WAMY, Hisham Muhammad, ya ce ƙungiyar ta kawo tawagar likitoci sama da 30 daga sassa daban-daban na duniya domin gudanar da aikin tiyata na tsawon mako guda a jihar.

Ya ce tawagar, ƙarƙashin jagorancin babban likitan tiyata, Dakta Abdul Latif Barnawi, ta ƙunshi ƙwararru a fannoni daban-daban, ciki har da tiyata , lafiyar mata da haihuwa, da tiyatar yara.
A cewarsa, ana sa ran marasa lafiya kusan 1,500 za su amfana da tiyatar kyauta da sauran ayyukan kiwon lafiya, ciki har da samun magunguna da kulawar bayan tiyata.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
