Labarai
Gwamnatin Kebbi Za Ta Kafa Kwamitin Kula Da Jin Daɗin Ma’aikata
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na inganta walwalar ma’aikata, inda ya sanar da shirin kafa kwamiti domin tsara hanyoyin kula da jin daɗinsu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin buɗe wani taron horaswa na kwana biyu kan amfani da tsarin gwamnati na zamani ta hanyar fasaha domin inganta ayyukan gwamnati, wanda aka gudanar a Birnin Kebbi.
Ya ce kwamitin zai duba shirye-shiryen tallafa wa ma’aikata da suka haɗa da rancen gidaje, babura da sauran tallafe-tallafen da za su inganta rayuwarsu.
Nasir Idris ya bayyana ma’aikata a matsayin ginshiƙin gwamnatinsa, tare da yabawa ƙungiyoyin ƙwadago da ma’aikatan gwamnati bisa goyon baya da biyayya da suke bai wa gwamnati.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa walwalar ma’aikata fifiko, yana mai cewa jihar Kebbi na daga cikin jihohin da ke biyan albashi, fansho, kuɗaɗen ritaya da hakkokin mamata a kan lokaci.
Gwamnan ya kuma tunatar da cewa Kebbi na daga cikin jihohin farko da suka fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa, yana mai cewa tsarin albashin jihar na daga cikin mafi kyau a Najeriya.
Haka kuma ya sanar da shirin samar da hasken rana a dukkan sassan sabon sakatariyar gwamnatin jihar mai suna Bola Ahmed Tinubu domin samar wa ma’aikata yanayin aiki mai kyau.
Tun da farko, shugaban ma’aikatan gwamnati na jihar, Malami Shekare, ya ce taron horaswar wani muhimmin mataki ne na zamani domin inganta aikin gwamnati ta hanyar fasahar zamani.
Shi ma kwamishinan ƙirkire-ƙirkire da tattalin arzikin zamani, Ibrahim Muhammad Sakaba, ya ce shirin zai taimaka wajen koya wa ma’aikata dabarun amfani da fasaha domin gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.
Sani Haruna/Kebbi
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
